TAMBAYA TA 015


*HUKUNCIN YIN ALKUNUTU SABODA CUTAR CORONA ?*

*Tambaya*
Assalamu Alaikum
Meye hukunci yin Alkunut saboda Annobar coronavirus ?

*Amsa*
Wa alaikum assalam

Babu nassi bayyananne yankakke wanda yake nuna ana yin Alkunutu idan cuta ta yadu a gari, saidai Malaman Shafi'iyya da Kuma wasu daga cikin malaman hanafiyya da Hanabila suna ganin Mustabbi ne yin Alkunutu idan ciwo ko bala'i ya sauka, ya kuma gama gari saboda Annabi (SAW) ya yi Alkunutu ga abokan gaba lokacin da suka kashe makaranta Alqur'ani, ita ma Kuma gama-garin cuta idan ta sauka a gari tana jawo rasa rayuka da dukiyoyi, hakan sai ya nuna hukuncinsu daya.
Sannan lokacin da Annabi SAW ya zo Madina ya samu wasu cututtuka a cikinta har wasu Sahabbai ma sun harbu kuma ya yi addu'a Allah ya dauke su, hakan sai ya nuna ana iya yin addu'a saboda neman dauke Musiba, ita Kuma Alkunutu addu'a ce.

Don neman karin bayani duba Almugni (2/115) da Al'ashbahu wan naza'ir na Ibnu Nujaim (372) da Mugni Almuhtaj (1/242) .

Zance mafi inganci shi ne za'a iya yin Alkunutu saboda CoronaVirus, yawancin Musibu Zunubai ne suke kawo su, Istigfari da kan-kan da kai Kuma yana kau da Bala'o'i da cututtuka kamar yadda Allah ya yi bayani a suratus Safat a kissar Annabi Yunus da Kifi.

Saidai ya wajaba a guji taruwa da yawa a guri daya, saboda cuta ce mai fantsama, kuma ana iya daukarta a lokacin cinkoso kamar yadda Likitoci suka tabbatar, ya halatta mutum ya yi Alkunutu shi kadai.

Allah ne Mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

29/03/2020

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)