Darasi daga Rasuwar Abba Kyari!
Mansur Sokoto
Assabar 24 ga Sha'aban 1441H (18 ga Afril 2020)
Babu shakka rasuwar wannan bawan Allah ta kidima
ni matuka.
Mutum ne ba mai yawan magana ba. Masu sukar
sa da masu yabon sa duk ba su iya kawo
kalaminsa. Yau da gobe za ta bayyana alherinsa ga
Najeriya ko Sharrinsa.
Muna yi masa fatar alheri; ya mutu Musulmi kuma a
Jum'ah babbar rana. Sannan ya mutu a sanadiyyar
Annoba wadda Annabi (S) ya ce, Allah yakan mayar
da ita Rahama ga mumini.
Yanzu dai ta kara tabbata; wannan Annoba gaskiya
ce. Ko mu dauki matakan da suka dace ko kuma
mu yi da-na-sani a nan gaba.
Hasashen da Turawa suke yi ma nahiyarmu ta Afrika
shi ne za ta zama cibiyar wannan annoba ta duniya
in da Miliyoyin mutane za su mutu a sanadiyyar ta
kamar yadda ya taba faruwa a kimanin shekaru 102
da suka wuce. Muna da hanyoyi biyu na hana
aukuwar haka:
1) Dagewa ga addu'a tare da sadaka (Maganin
musiba).
2) Daukar matakan kariya da masana suka ayyana,
musamman kulle garuruwanmu kuf, sannan mu kula
da tsaftar jiki da ta muhalli da nisantar taruwar
jama'a wuri guda.
Shawarata ga Malamai da Shugabannin
kungiyoyin addini, don taimakawa wajen dakile
yaduwar wannan cuta ita ce, a dakatar da Sallolin
Tarawihi a azumi mai zuwa. Haka su ma majalisan
Tafsiri a duk fadin kasar nan. A maimakon haka ayi
amfani da kafofin sadarwa don isar da sakon Allah
ga mutane.
In da ba a sanya dokar hana fita ba mutane su
saurara ma musabaha da hannu, kuma su rage
cushewa a wuri guda a Masallaci da Kasuwa da ko
ina.
Mu tuna, Allah _subhanahu_ ya ce: *"Ya ku
wadanda suka yi imani ku rika yin hattara da
sauna"* Suratun Nisa'i: 71. Don haka, mumini shi ne
wanda yake riko da sababi sannan ya dogara ga
Allah.
Allah ya jikan Abba Kyari da duk Musulmin da suka
rasa rayukansu a cikin wannan annoba, ya sa ta
zama rahama a gare su. Allah ya yaye ma duniya
wannan musiba.