JIKIN ƊAN ADAM 07


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 07🍍🍊*

*(Fitowa ta Bakwae)*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Dabino dan bishiya ne da al'umma da dama suka san shi, abu ne mai daraja masamman ma da yake ya qumshi kusan duk abincin da dan adam yake buqata, yana da tsohon tarihin da wasu 'ya'yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun a da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan bishiya, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zaqin ya shafi bosasshe da danye wanda ya nuna.

Ana qimanta zaqin sukarin da dabinon ya tattara wajen kashi 78-70 cikin dari na abubuwan da dabinon ya qumsa, kuma wannan sukarin na dabino nan take yake narkewa a cikin jini sabanin sauran 'ya'yan bishiya, a nan ne za mu ga hikimar muslunci ta sanya dabino ya zama abin farko da mai azumi zai fara ci, wannan don a dawo masa da abubuwan buqatar da ya rasa ne cikin gaggawa, Allah Mai Girma ne a dukkan lamarin Sa.

Wata malama mai zurfin ilimi a bangaren kayayyakin abinci a Jiddah, wato Prof. Waddaha Mohammed tana cewa: Cin qwayan dabino guda goma mai nauyin 100g zai iya samun abubuwa na amfani gwargwadon lissafin da Amurka ta bayar ga matasa wadan da take cewa a ciki:- Wanda yake cin dabinon a kullum kamar yadda muka fado zai sami duk abin da yake buqata na Magnesium, Manganese, copper, zai sami kusan abin da yake buqata na rabin sinadaran Potassium da calcium.

Bawannan kadai ba akwai ma 75g na carbohydrate, 63g na sukari, 8g na Dietary fiber, 0.4g na Fat, 2.5g na Protein, 21g na ruwa,0.262 mg na Manganese, 1.32 na minerals, abin da Prof. Waddaha ta ce: Bushasshen dabino ya qumshi: Carbohydrate 79.6%, Fat 2.5%, Water 33%, Minerals 1.32%, Dietary fiber 10%, sai Vitamins A, B1, B2 da C, kamar yadda ya kuma ya qumshi abubuwa da dan dama, a taqaice in ka duma dabino shi kadai ya isa ya zama abincin da zai gina jiki in ba don tsoron a yi masa cin qoshi ba.

Bincike ya nuna cewa dabino ya qumshi: Minerals, Calcium, Protein, Fat, Lime, Coramine, Dietry fiber, Phosphor, Chlorine, Manganese, Potassium, Copper, Vitamin C, da Magnesium da wannan za mu gane cewa dabino ya qumshi manya-manyan abubuwa na abinci, wadan da za su gina jiki da jijiya, sukuma bayyana wa mutum matasantarsa ko da kuwa ya dan kwana biyu, da za a hada dabino da madara tabbas abinci ne mai kyawun gaske, masamman ga wanda yake da matsalar ciki.

Masana suke cewa: In don kwatanci ne abincin da yake cikin dabino yana daidai ne da na wani nau'i na nama, ko ribi uku na kifi, yakan amfanar da masu cutar fatarar jini, wasu cututtuka da suka shafi qirji kamar yadda ake kwaba shi a dafa a riqa sha daidai gwargwadon yadda aka nuna wa mutum, tamkar dai yadda yake amfanar da qananan yara, matasa, 'yan wasa, ma'aikata, ramammu, da mata masu ciki, dabino yakan taimaka wa masu matsalolin ido, gaba daya, kamar dai yadda yake taimakawa wajen qara gani, da qara qarfin kunne, yakan natsar da mutum ya yi masa maganin saurin hawa sama ko fada da mutane, shi ya sa ake son mutum ya niqe shi ya hada da madara ya sha da safe.

Dabino yakan tausasa jijiyoyi masu dauke da jini, ya gyara uwar hanji, ya yi mata maganin radadi da rauni, sannan yana taimaka wa qwaqwalwa sosai ba kadan ba, kamar dai yadda yakan taimaki maza wajen ba su kuzarin shimfida, dabino yana taimaka wa masu azumi da tashin wadan da suka dan kwana biyu, yakan kuma taimaka wajen niqe abincin da aka ci, ya ba mutum yin fitsari sosai don fitar da cuta, ya tsarkake masa hanta, ya wanke masa qoda, niqaqqensa kuwa yakan yi maganin tari, da majina.

In aka qara masa kwakwa da madara a lokaci guda yakan qara masa qarfin aiki ba shakka, abu ne mai kyau matuqa, ba a hana mutane cin dabino in wadan da suke da qibar gaske ba, ko masu fama da cutar sukari, kamar danyen dabinon wanda ake ganin kamar ya fara rubewa ba ruba ba ce kyawunsa kenan sunansa rudab /rutàb/ yana ta taimakon mace wajen haihuwa da wuri, ya taqaita zuban jini, sannan sukarin dake cikinsa yakan taimaka wajen dawo wa mace da qarfinta.

Da wadannan bayanan za ka fahimci cewa komai amfanin dabino a matsayin abinci, a gefe guda kuma magani ne, yawaita cinsa ba tare da qa'ida ba zai iya haifarwa mutum da abubuwa da dama, ko in mutum yana da wata cutar ya dagar masa, kamar dai cutar sukari, hawan jini, zarcewar qiba, ko mata masu ciki su barar da shi, yana da kyau mace mai ciki ta kiyayi yi wa dabino mummunan ci, don kar ya ba wa mahaifa qofar da za ta fitar da abin da yake cikinta.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله 
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته

*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*
Post a Comment (0)