SALLAR ISTIKHARA DA HUKUNCE-HUKUNCEN TA 06

🔹 *ISTIHARA DA HUKUNCE~HUKUNCEN TA* 

*06* rubutu na Karshe 

→Shin ya halatta a maimaita Istihara a kan al’amari daya?
.
.
 Sallar Istihara tana kama da Sallar Rokon Ruwa ta hanyar kasancewa Sallah ce ta wata bukata, kuma tana kama da ita ta hanyar kasancewa Sallah ce da take harde da addu’a. Wannan nau’i na Sallah yana kama da addu’a ta wata surar. Idan aka hada haka da ma’anar Sallah bisa lugga wadda ke nufin addu’a, malamai suna ganin yawaita yin addu’a abin so ne, don haka suna ganin babu abin da zai hana a rika maimaita ta.



Sheikh Adanan Ar-aur ya ce, “Fadin wadansu ’yan uwa na kada a maimaita ta saboda kasancewarta addu’a kebantacciya a karshen wata Sallah kebantacciya, ba zai hana a maimaita ta ba. Domin hakan ba ya daga cikin babin kirkirar wani abu, kuma idan ya kasance haka, ya halatta a maimaita ta saboda rashin hani kan haka. Kuma da a ce Sallar Isithara ta kasance ma’abuciyar wani sababi ne kawai da sai mu ce ba za a maimaita ta ba. Amma kasancewarta Sallah ce ta haja (neman bukata) ya sa ta fi kusa da addu’a fiye da wanin wannan. Don haka muka rinjayar da maganar wadanda suka ce za a iya maimaita ta. Allah ne Mafi sani.” Kuma daga cikin wadanda suka bayar da fatawar halaccin maimaita ta a wannan zamani akwai Sheikh Abdul’aziz bin Baz da Sheikh Muhaddis Nasruddin Albani, sai dai shi ya yi kaidi ga maimaitarwar bisa cewa in mutum bai samu natsuwa a sallarsa ta farko ba ne.

Daga cikin wadanda suka amince da maimaita Sallar Istihara, har ma suka mustahabbantar da haka, akwai Alhafiz Al-Iraki, kuma Shaukani ma ya tafi kan wannan fatawa a cikin littafinsa Nailul Audar. Har ma ya kafa hujjar maimaitawar da cewa ya kasance “idan Annabi (SAW) zai yi addu’a yana yi ne sau uku.”

Sannan ya zo a cikin Sahihu Muslim cewa lokacin da aka kona Ka’aba, Abdullahi Bin Zubair (RA) ya ce, “Da waninku za a kona masa gida ba zai yarda ba, sai ya sake gina shi. To yaya kuma ga dakin Ubangijinku? Lallai ni zan yi Istihara sau uku, kuma in himmantu ga al’amarina (na sake gina Ka’aba).”

Wannan yana nuna karfin rinjayen maimaita Istihara a kan rashin maimaita ta.

Amma masu kafa hujja da Hadisin Anas da ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya Anas idan ka himmantu da wani al’amari ka yi Istihara ga Ubangijinka sau bakwai.” Wannan Hadisi ne mai rauni kwarai, hafizan Hadisi sun hadu kan rauninsa.

Imam Annawawi ya ce: “Isnadinsa garibi ne, a cikinsa akwai wanda ba a san shi ba.” A duba Azkar shafi na 111. Shi kuma Al-Iraki ya ce: “Hadisi ne sakidi (wani abu ya fadi daga cikinsa) babu hujja a cikinsa -Nailul Audar, Mujalladi na 3 shafi na 74. Al-Askalani kuma ya ce: “isnadinsa mai matukar rauni ne.” Fat’hul Bari, Mujalladi na 11 shafi na 187.

Shin Istihara tana da wani lokaci na musamman ne?

Istihara ba ta da wani lokaci na musamman da ake yin ta ko aka kebance domin yin ta. Ana iya yin ta a kowane lokaci. Amma idan mutum ya kintaci lokacin da aka fi karbar addu’a babu laifi, saboda abin da ya gabata cewa Sallah ce da kuma addu’a ta neman biyan wata bukata.

Daga cikin lokutan da malamai suka rinjayar na karbar addu’a, akwai lokacin da ke tsakanin kiran Sallah da Ikama da lokacin da ruwan sama ke sauka da sulusin karshe na dare da sa’a ta karshe na ranar Juma’a da lokacin da mutum ke tafiya da kuma daren Lailatul kadar.

Sai dai abin tambaya shin ya halatta a yi Sallar Istihara a lokutan da aka hana nafila? Kuma wadanne ne lokutan?

Asali dai an hana yin Sallar nafila a wasu lokuta. Sai dai malamai sun samu sabani kan yin salloli ma’abuta sabubba a lokutan hani.
Abin da yake daidai, halaccin yin irin wadannan salloli a wadannan lokuta, kamar Sallar Tahiyyatul Masjid da Sunnatu Wudu da Sallar Istihara, musamman idan lokaci ya kuntata masa ko yana cikin matsuwa.

Sai dai da za a bar yin Sallar Istihara a wadannan lokuta da zai fi nisanta daga haifar da sabani, kuma a fi samun natsuwa, saboda Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ka bar abin da kake shakka zuwa ga abin da ba ka shakka.”

Lokutan hanin sun hada da bayan Sallar Asuba har sai rana ta bayyana ta daga sama da lokacin zawali - lokacin daidaituwar rana a sama- har sai ta karkata da lokacin da ta yi fatsi-fatsi har sai ta fadi.

A sani, ba a iyakance lokacin da ake umartar mutum da yin Istihara ba, iyaka dai da ya himmantu ga aikata wani abu sai ya yi Istihara, ya yi niyya ya yi nufi kuma gabanin ya aikata wannan abu da yake so, saboda fadin Manzon Allah (SAW); “Idan dayanku ya himmantu da wani al’amari...”

Idan mutum ya fara yin wasu abubuwa, amma bai samu wani abin ba, ya halatta ya yi Istihara matukar dai bai cimma manufarsa ba, idan Istiharar ta kubuce masa sai ya yi addu’ar alheri, ya roki Allah Ya kawo masa alheri kuma Ya kare shi daga sharri.

Wannan shi ne dan abin da ya samu dangane da wannan babi mai muhimmanci. Allah Ya sa abin da muka fada ya zamo alheri gare mu. Kura-kuranmu, Allah Ya yafe mana.

Wasallallahu alan nabiyyil karim wa alihi.

Salihu Is’hak Makera
Gabatarwa:- Salis kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

2 Comments

Post a Comment