JIKIN ƊAN ADAM 08


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 08🍍🍊*

*(Fitowa ta Takwas)*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Kankana daya ce daga cikin 'ya'yayen bishiyoyi masu zaqi da suke yi a lokacin bazara, sai dai yanzu kusan ana samunta a kowani yanayi ma, tana cikin 'ya'yayen bishiya da ba sa yankewa, irin su lemo, an fara sanin Kankana ne a qasashe masu zafi irin su Afrika da India, kafin ma su tsallaka zuwa qashen dake zagaye da tekun tsakiya wato Mediterranean, daga nan sai ta qarisa Europe da kudancin Amurka.

Wani abin da zai ba ka mamaki shi ne ba duk masana ne suka amince da cewa kankana dan bishiya ce ba, wasu daga cikin manya-manyan masu bincike suna ganin cewa ana sakata a cikin ganyayyaki ne kamar su Cucumber sai dai tana da zaqi, ana samunta a ko'ina cikin nau'uka da launuka mabambanta, wanda har jami'ar Washington dake Amurka ta fitar da wasu alqaluma inda take cewa akwai nau'o'in kankana a duniya har 126 dukkansu suna dauke ne da nau'o'i kala daban-daban.

Kankana kusan dukkanta ruwa ne don gwargwadon ruwan dake cikinta an qiyasta ya kai 90%-99%, sukarin dake cikinta kuwa zai kai 8%, sannan ana samun vitamin C da vitamin B a cikinta, kamar yadda ta tattara sinadarin Sulphur, Calories, Phosphor da kuma Potassium, wani kuskure da wasu suke yi shi ne suna cire 'ya'yan kankanan a lokacin da suke sha, ba su san cewa kamata ya yi su tauna ba, 'ya'yan ba su da daci sai dandanon mai dadi ga Fat 43%, Sugar 16%, sai Protein 27.

Duk da cewa akwai kankana kala daban-daban a duniya amma ku san dukkansu suna da sinadaran qara kuzari (wato Vitamins) da sauran ababan gina jiki kamar Protein, Calcium, Iron, Sodium, Magnesium, Phosphor, Potassium, da kuma sauran Vitamins A, da C, zai yi kyau mu waiwayi wasu fa'idojin da kankanar ke yi ga lafiyar dan adam.

QODA: Kankana takan taimaka wa qoda matuqa, domin ruwan dake cikinta, kamar dai yadda aka sani takan sauqaqe wa taruwar fitsari da fitarsa, wannan sabo da tana da sinadarin Potassium wanda yake taimakawa wajen korar gurbataccen sinadari daga jukkunammu, sannan sinadarin yana rage yawan sinadarin Hyperuricemia a cikin jini.

FATAR DAN ADAM: Dangane da fatar da adam, sananne ne cewa kankana tana da sinadarin da yake kare jikin dan adam daga Oxidation, don haka ne ma take iya fatattakar tsattsakar fata, da lalacewarta, takan ba wa fata kariya daga hasken rana mai cutarwa, masamman yadda take dauke da sinadarin Lycopene da Crotin wadan da suke taimakawa wajen kare jikin dan adam daga qunar ranar da take sanya cutar fata ko koma cancer wace take samun fatar.

HAWAN JINI: Sai kuma mutane masu fama da mummunar bugawar jini, kankana takan taimaka musu sabo da tana qunshe da sinadarai kamar su Manganese da Potassium masu aiki wajen tsara bugawar jinin, matuqar kankana ta qumshi wadannan sinadaran kenan ta dace da mutum mai fama da hawan jini ya riqe ta a matsayin qari cikin abincin da yake iya ci a kullum.

CIWON SUGAR: Kamar dai yadda muka fadi ne a baya cewa kankana ta qumshi sinadarin Potassium da Magnesium wadan da aikinsu shi ne taimaka wa jiki wajen tato sinadarin Insulin wanda yake tsara wa sukari yadda zai yi aiki a cikin jini, qarancin wannan sinadari shi yake hana iya sarrafa sinadarin Glucose da mutum ya samu a jikinsa ta hanyar wasu abinci masu masifar zaqi, ko wurin wasu 'ya'yayen bishiyar, a nan cin kankanan zai taimaka wa mai cutar ko ta ba wa wanda bai da ita wata kariya.

KUZARIN JIKI: Ana aiki da kankana a matsayin wata madogara ta dabi'a wace take maye makwafin wasu magunguna masu qara wa mutum kuzari a jiki da qarfi da lafiya, wadan da galibin 'yan wasan motsa jiki su suke amfani da su, domin kankana tana da dauke da Potassium da Magnesium da kuma Vitamin B da nau'o'insa wanda shi kuma yake qara kuzarin jiki.

MATSALOLIN IDO:

 Kankana takan taimaka wa ido wajen kare ganin mutum, don tana dauke da Vitamin A wanda yake da mahimci ga idon mutum, wani bincike ya gano cewa in dai mutum zai sanya kankana a gaba kullum zai ci na kimanin yankar N100 a yau, to ba ko shakka kankana za ta taimaka masa wajen kyautata ganinsa masamman domin wadan da ganinsu yake raguwa a dalilin aiki da na'urorin zamani kamar su talabijin, wayoyi da kwafyuta, ko kuma don tsufa.
BA SHI KENAN BA.

Zamu ci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله 
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته

*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*
Post a Comment (0)