*KHUÆŠUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:*
27/J-TSANI/1441-HJRY
21/FEBRARY/2020-MLDY
🎙️GABATARWA Abubakar BN Mustafa Biu
♦️TOPIC [KINDNAPPER➖SHIRYA YIN SHARI'A DA ALLAH]
➖NA KASASHI GIDA 8
1_ MUQADDIMA
Yaku bayin MAI RAHAMA- muji tsoron MAI RAHAMA don samun yardansa, da samun yardansane ake samin jin daÉ—in dindindin, ake samun albarka cikin dukiya da iyalai da 'ya'ya, Albishir na kyakkyawar karshe ga wanda yakaÉ—aitashi yabauta mishi
2_ HADISIN ANNABI SAW
ANNABI SAW yace➖ALLAH SW yace "Mutum 3 nine zanyi kararsu kuma inyi shari'a dasu a kiyama, kuma duk wanda nayi shari'a dashi zanyi galaba akansa, ¹Mutuminda yabayar donni sai yayi yaudara, ²Mutuminda yasayarda É—a yaci kuÉ—insa, ³Mutuminda yabawa lebura aikin yakammala aikin sai yaÆ™i bashi haƙƙinsa, (BHR-2227, 2270 & IBN MAJAH-2442)
3_ MA'ANAR NAU'I NA 1
(Mutuminda yabayar donni sai yayi yaudara) Cikin TAHQIQIN YASIR RAMADAN da MUHD IBN ABDLH ga SUNAN IBN MAJAH, suce= wato yayi alkawarin bayarda agaji don addinin sai yaƙi bayarwa, wannan akwai babban shari'a tsakaninsa da ALLAH SW
4_MA'ANAR NAU'I NA 3
(Mutuminda yabawa lebura aiki yakammala amma yaƙi bashi haƙƙinsa) ƙodago (leburanci) aikine mai muhimmanci harma ANNABAWA sunyi,
Surukin ANNABI MUSA ALSLM yace masa <<inason in aurama É—aya cikin 'ya'yana sadakin shine kayimin leburanci na shekaru 8>>
kaga halaccin kodago don samun abinci da aure,
ANNABI SAW yayi kodagon kiwon tumaki ga Quraishawa kafin ANNABTA suna biyansa kuɗi dasu yake biyan bukatunsa, don haka danne haƙƙin lebura ko bala'ine ALLAH dakansa zaibi masa kadunsa,
Wannan a zamanin yau ya shafi gomnanda yahana Ma'aikata albashi ko yaƙi biyan waɗanda sukayi ritaya bayan kammala shekaru 35 suna aiki,
5_ MA'ANAR NAU'I NA 2
(Mutuminda yasayarda bawa yacinye kuɗinsa) A wata ruwaya 💡ANNABI SAW yace "Mutum 3 ba'a karɓan sallarsu, ciki akwai wanda yabautarda ɗa"
◼️IBN HAZM ya naÆ™alto cewa= ada ana sayarda É—a don biyan bashi sai ALLAH SW yahana kuma madadin hakan sai yace<<idan me bashin yana cikin matsi a saurara masa zuwa walawala, idan kun sadakarma tafi alhairi>> {SRT BQR}
.
.
6 TA'ALIQI AKAN NA
Yaku bayin ALLAH! a wannan zamanin zamu iya ƙiyasin (Sayarda ɗa a matsayin bawa) da (KINDNAPPERS) wato masu satan mutane a hanyoyi, tituna, gonakai, ƙauyuka, birane har cikin gidaje don neman kuɗin fansa, su ɗauke ɗa ba bawaba, suyi ciniki da danginsa yadda ake cinikin bawa su kallafa musu kawo dubunnai ko miliyoyi kafinsu sakeshi, wasu dangin harma gwanjarda kayan abinci da dabbobi da plotai harma da gidaje sukeyi don haɗa kuɗin fansa in ba hakaba a kasheshi, INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
NA RANTSE DA ALLAH WANDA RAINA YAKE HANNUNSA➖WaÉ—annan Mutanen ALLAH SW da kansa zaiyi shari'a dasu aranar QIYAMA, ALLAH ne mai Æ™ara domin shi suka yiwa laifin kuma shine AlÆ™alinda zai yanke musu mummunar hukunci
Domin sun maida É—a bawa sukayi cininkinsa suka ci kuÉ—in
◼️IBNUT TEEN yace= ALLAH SW zai gurfanarda dukkan azzalumai yahukuntasu a Æ™iyama, amma ya ware waÉ—annan ukun da ambato ya ayyanasu domin nunawa duniya zai tsananta musu hukunci da azaba samada kowa, (FAT'HUL BAARY)
7_ƘIRA
Yaku KINDNAPPERS da BOKO HARAM da DUKKAN 'YAN TA'ADDA cikin 9jry da wajenta- kuji tsoron ALLAH kubari kuma ku gaggauta tuba ku koma gareshi tun kafin kufaÉ—a tarkon ALLAH SW na Mutuwa
ALLAH SW yace <<Yaku bayina da sukayi ɓarna abisa kawunansu kada kuyanke tsammani daga rahamar ALLAH, ALLAH yana gafarta zunubbai gaba ɗaya (ga wanda yatuba) ALLAH Mai Gafarane Mai Jin ƙaine>>
.
.
8,RUFEWA
Yaku 'yan uwa- musammanma mutanen BORNO- Ku amsa kiran Mai girma GOMNA ZULUM (KHADIMUL UMMAH) na zaiyi azumi litinin mai zuwa da niyyar samun zaman lafiya da rugujewar boko haram da sauran 'yan ta'adda,
YA RABBANA KATSARE MANA DR ISA ALI PANTAMI DA DUKKAN MALUMANMU DA JAGORORINMU DA DUKKAN AL'UMMANMU daga kaidin dukkan Makirai
.
.
YA ALLAH! KARUGUZA SHEKAU DA DUKKAN NAU'IKAN BOKO HARAM DA MASU FASHI DA GARKUWA DA MUTANE DA DUKKAN WADANDA SUKA HANA ƘASARMU ZAMAN LAFIYA
AMIN
_# Abubakar BN Mustafa Biu_
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```