AURE RAHAMA NE


Aure Rahma ne, samun da albarka ne. Duk Wanda ALLAH yayi masa baiwa da samun haifuwa to ya godewa ALLAH tare da nuna farin ciki da wannan kyauta Mai girma.

Kuma mu sani kowanni da nada hakki Akan iyayen sa tun daga sanya masa suna Mai kyau da ma'ana tagari, kula dashi wajen yi masa addu'a, ciyarwa, tufatarwa, ilmantarwa, horo in ta Kama da koya masa Sanaa da zaman duniya.

Hakika tsatso yana naso, wato in duhu ya doki duhu to zaa samu baki kirin. Ma'ana Ana gadon halitta da Hali na iyaye, don haka matakin farko na tarbiyya shine samarwa da Uba nagari, da uwa tagari. Ana son addu'a da Neman zabin ALLAH wajen aure, da bin tafarkin Annabi saw wajen zaman iyali na addu'oin ma'aurata, da yin addu'a yayin da ciki ya samu har zuwa haifuwa, daga nan sai sanya Ido da dagewa wajen cusawa Yara tarbiyyar addini, da kula da ruhi da ganganci jikin Wanda ake tarbiyya.

Zai yiwu ba zaka samu rayuwar zama da iyalan ka har su girma kana da rai ba, haka nan iyaye mata, to mu sani ALLAH yana Jin kan zuryar bayin ALLAH na kwarai, wato a kula masa bayan sa bayan baya duniya.
Samun kangararru cikin iyali ga Mai kokarin kula da addini da kiyaye matakan tarbiyya jarrabawa ce, sai mu tuna Annabi Nuhu da Annabi Lut. Mafita shine komawa ga Allah da koya masu addini. Hakanan ALLAH na iya fitar da haske daga duhu a samu zuriya ta gari daga iyaye masu sakaci.

Da kowa na sauke hakki da nauyin da ke Kansa na tarbiyya da tarbiyyar mu da iyalan mu tafi haka inganci da nagarta. Kuma da hukumomi na kulawa sosai da gyaran tarbiyya da dukkan matsalolin mu a kasar nan sunyi sauki.

ALLAH baya kuskure, don haka duk abinda ya Baka sai ka gode ka kula. Abinda ya gyara al'ummar baya shi zai gyara al'ummar yanzu don haka hukuma, malamai da iyaye sai mu kula. Kuma ka fara gyara da'a da tarbiyyar ka da kanka Kafin ka gyara wadan su.
Post a Comment (0)