KINA DA MUTUNCI, TO KAR KI ZUBAR DA SHI


🌻 KINA DA MUTUNCI, TO KARKI ZUBAR DA SHI 🌻

Karki kuskura ki yarda ki biye masa kuje kuyi murnar ranar shedancin nan ta VALENTINE da sunan wai ranar masoya. 

Domin fitsaranci ne tsantsa acikin lamarin, ki tsare mutuncinki karki zama ballagaza.. 

 Za ki iya cewa ai ko kunje wajan, zaki iya tsare mutuncinki bazaki yarda ayi ta'adi da ke ba. 

"Yer uwa, kawo kunnenki kiji.... shi fa Dakalin soyayya akwaishi da santsi, idan kika hau bazakisan lokacin da zaki rikito ki afko cikin Haramun ba, 

Maganin haka kawai shine karki yarda kije ko ina da wani, kuma ba ruwanki da nuna murnar, saboda da muguwar rawa gwamma kin tashi.

 Domin akwai wasu mazan wadanda sun iya dadin baki da yaudara, tayadda zai yaudareki har ki amince da mummunan niyyarsa, ke kuma gudun karki batawa masoyinki rai, saboda yau ce ranar masoya ko.. 
.
Kkinaso kibaiwa fulawar soyayyarku ruwa, domin kara samun gurbi acikin zuciyarsa ko? 

 A gefe daya kuma kin yarda ki kyatawa kanki mutunci, kinyarda ki sabawa Ubangijinku domin farantawa Bawansa rai ko... 

 Wallahy kisani cewa : a ranar da kika amince masa, ranar da kike ganin ai babu abinda zai faru, kuma ko ma ya faru ai akwai *Abortion* ko?  

To kiji da kyau : Idan Allah yaga dama sai ayi ayi amma yaki zubewa, kinga anan kam kin kirawowa kanki ruwa kuma kin zubarwa da kanki mutunci, kin zubarwa da gidanku da iyayenki mutunci a cikin rana daya. 

 Wata kila ke Ustaziya ce ko mai mutunci ce a unguwarku, ana daraja ki, ana mutunta ki kuma ana karrama ki, gidanku gidan daraja ne da mutunci, to karki Bari ki zubar da mutuncinki a wajan Allah da kuma idanuwan Al'umma. 

 Karki bari wasu wawaye su kaiki su baro, saboda kwadayin wata dauda a duniyance, su lalata rayuwarki, Wallahy ke zasu bari da jigilar kayan kunya, kuma ita soyayyar wacce a sanadiyyarta ne hakan tafaru, to daga ranar zakiga ya gogeki acikin tsarin masu mutunci da tunani.  


Ya gama yaynki saboda ya samu abinda yakeso Daga gareki, 

Yanzu wa gari ya waya? Allah yakara tsare mana imaninmu kuma yarufa mana Asiri duniya da lahira. 


✍🏻 Dan uwanku a musulunci 
Idris M Rismawy
Post a Comment (0)