KUKAN KURCIYA

*Kukan Kurciya 🐦*


Wasu daga cikin tsuntsaye masu wayau su kan bi kwararo-kwararo don tsintar ragowar sigarin 🚬 da mutane suka sha suka jefar, suna yin amfani da wannan ragowar sigarin wajen zagaye sheqarsu da shi a matsayin maganin 'kwari (insecticide), domin sigari tana ďauke da sinadarai ne guda uku: *Nicotine, Tar* da kuma *carbon monoxide,* waďannan tsuntsaye sun gano cewa qonannen sinadarin *nicotine* da yake a sigari yana illatar da 'kwari masu cutarwa kamar su *gara, 'kwar'kwata* da sauran 'kwari masu tashi *(qudaje)* da sauransu, wannan sinadarin sai ya zama kariya ne suka ba wa sheqarsu da abincin da suke adanawa da jariransu daga waďannan 'kwari. 
.
Idan har tsuntsaye za su fahimci sigari a matsayin guba mai cutarwa, to ina ga mu mutane masu hankali da tunani? 'Yan uwa mu nisanci shan sigari domin tana raunata lafiyarmu. 
.

Allah Ya ganar da mu 👏🏾
.

*✍🏾Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*
.

https://www.facebook.com/896785910406825/posts/2771375662947831/?app=fbl


Post a Comment (0)