*IDANN AKA SAMU SABANI TSAKANIN MATA DA MIJI A ADADIN SAKI, MAGANAR MIJI ITA CE GASKIYA !*
Tambaya
Assalamu alaikum, Malam mace ce ta zo gida ta ce mijinta ya sake ta saki biyu, shi kuma ya ce saki daya ne, to malam maganar Wa za’a yi amfani da ita a cikin su?
Amsa
Wa alaikum assalam, To dan’uwa idan aka samu sabani tsakanin miji da mata a siffar saki ko adadinsa, to maganar miji ita za’a gabatar, saboda a hannunsa sakin yake, yana daga cikin ka’idoji tabbatattu a Fiqhun Musulunci:
“من كان القول قوله في أصل الشيء، كان القول قوله في صفته وما لا فلا”.
Duk Wanda maganarsa abin dogaro ce a tushen abu, to maganarsa ita ce abin Dogaro wajan bayanin sifar abin, wanda kuma ba haka ba ne, to ba haka ba ne.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
02/01/2020
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```