Maganganu Da Ayyuka Da Suke Kore Tauhidi Ko Kuma Su Rage Shi.
A wannan babi akwai fasali fasali kamar haka: Fasali Na Farko: Da’awar sanin ilimin gaibu wajen duba hannu ko kasa ko taurari.
Fasali Na Biyu: Sihiri (Asiri) da bokanci da kuma duba.
Fasali Na Uku: Gabatar da hadayoyi da masu neman kusanci da masu alwashi suke yi a wurarn ziyara da kabarburuka da kuma girmamasu.
Fasali Na Hudu: Girmama mutum mutumi da kuma kafe shi domin tunawa da shi.
Fasali Na Biyar: Izgili da addini da kuma wulakantar da alfarmarsa.
Fasali Na Shida: Hukunci da abinda Allah ba shi ya saukar ba.
Fasali Na Bakwai: Da’awar cancantar shar’antawa ko halastawa ko haramtawa.
Fasali Na Takwas: Shiga kungiyoyin Ilhadi da kuma kungiyoyi na jahiliyyah.
Fasali Na Tara: Mahanga ta ci gaba a rayuwa.
Fasali Na Goma: Layu da kuma tofetofe.
Fasali Na Goma sha daya: Rantsuwa da wanin Allah da kuma tawassuli da neman taimako ga wani mahaluki da ba Allah ba.
Insha Allah zamuyi bayanin kowanne fasali dayan bayan daya, Amma inaga yau iya fasali daya zamuyi bayaninsa, idan Kuma Akwai sauran lokaci sai mu Kara fasali na biyu.
Allãh ta'ala yayi mana mai kyau*Fasali Na Farko:* Da’awar sanin ilimin gaibu wajen duba hannu ko kasa ko taurari da waninsu.
Abinda ake nufi da gaibu. Shi ne abinda ya boyu ga mutane na al’amuran da zasu faru a nan gaba da kuma abinda basa ganinsa, kuma hakika tabbas Allah kadaine ya kebanta da saninsa, Allah madaukakin sarki yana cewa: *“KACE: BABU WANI WANDA YASAN GAIBU A SAMMAI DA KASSAI SAI ALLAH KADAI”.* Suratun Naml, aya ta: 65.
Babu wanda ya san gaibu sai Allah mai girma da daukaka shi kadai, hakika kuma Allah yana tsinkayar da manzanninsa a abinda ya so na gaibinshi domin wata hikimarsa da kuma maslaha, Allah madaukakin sarki yana cewa: *“(SHI ALLAH) MASANIN GAIBINE, KUMA BAYA BAYYANAR DA GAIBINSA GA KOWA. SAIDAI KAWAI GA WANDA YA SO NA WANI MANZO”.* Suratul Jinn, aya ta:26-27.
Abin nufi ba ya tsinkayar da wani abu na gaibi sai dai kawai ga wanda ya zaba da isar da manzancinsa to sai ya bayyanar masa da abinda ya so ba gaibi, domin shi manzon zai kafa hujja da shi akan annabtarsa ta hanyar bayyanar da mu’ujuzozi wacce daga cikinta ba da labari na gaibi wanda Allah ya tsinkayar masa da shi. Wannan ko yana game manzo cikin mala’iku da kuma manzo cikin mutane, amma Allah ba ya tsinkayar da waninsu, su kadai kawai yake tsinkayarwa.Tho dukkanin wanda ya yi da’awar sanin ilimin gaibi ta kowacce hanya cikin hanyoyi in banda wanda Allah ya cire na manzanninsa tho shi tintirin makaryaci ne kuma kafiri ne. sawa’un ya yi wannan da’awar ta hanyar karatu a tafin hannu ne ko zane a kasa ko bokanci ko ta hanyar sihiri ko taurari ko ma wanin haka. Domin wannan ana samunshi wurin masu rufa ido da shaidanu na bada labarin wasu wurare da ba’a sansu ba ko ma wuraran da ba sa wannan wurin. Ko kuma bada rabarai na musabbabin wadansu cututtuka, sai su ce: wane ya aikata maka abu kaza-da-zaka wanda ya sa ka yi wannan rashin lafiyarne ta sanadiyyar haka, wannan fa anfanine da aljanu da kuma shaidanu, suke kuma bayyanawa mutane lalle wannan yana samuwane a gare su ta hanyar aikata irin wadan nan abubuwa don nuna yaudara da wayacewa…’
Shehul Islam Ibnu Taimiya yana cewa: “Su bokaye kamar kace dayansu yana da aboki a cikin shaidanu da ya ke ba shi labari na abinda ya shafi gaibu na abinda suke satowa na Magana, kuma sun kasance suna cudanya gaskiya da karya, hardai inda ya ce: “Daga cikin wadannan akwai wanda shaidani zai zo mishi da abinci, da kayan marmari da kayan zaki da wanin haka, irin abinda ba’a saminshi a wannan wurin.
Akwai kuma daga cikinsu wanda aljani yake tashi da shi zuwa Makkah ko Baitul makadis ko wasu wuraran”. Nan maganar Ibnu Taimiya ta kare.
Wani lokacin kuma bada labarin na su yana kasancewa ne ta hanyar anfani da taurari, wato lura da halayen falaki akan abubuwan dake faruwa a kasa, kamar lokacin tasowar iska, da zuwan ruwan sama da canzawar farashin kayan masarufi, da wanin haka na al’amuran da wai riya cewa suna saninsu ne ta hanyar taurari ta hanyar da suke gudana da kuma inda suke haduwa da kuma inda suke rabuwa, sai kuma ka ji suna cewa; duk wanda ya yi aure a lokacin tauraro kaza da kaza to abu kaza da kaza zai same shi, wanda kuma ya yi tafiya a tauraro kaza da kaza to abu kaza zai same shi, kuma dukkanin wanda aka Haifa a tauraro kaza da kaza to ciwo kaza ko abu kaza zai same shi, kamar yadda suke bayyanar da haka a wasu mujallu masa manufa akan irin wadan nan jagwalgwalo akan abinda ya shafi buruji da irin abubuwan da suke tafiya akansu.Wasu daga cikin jahilai da masu raunin Imani suna tafiya wurin wadannan masu harkar taurari sai ya tambaye su dangane da yadda rayuwarsu ta fuskanta, da kuma sauran irin abinda ke gudana akan haka na aurene ko wanin haka, to dukkanin wanda ya yi da’awar sanin ilimin gaibi ko kuma ya gasgata wanda ya yi da’awar sanin ilimin gaibin to hakika shi mushirikine kuma kafiri, domin yana da’awar tarayya da Allah a cikin abinda ya kebanci Allah shi kadai, su fa taurari abubuwa ne da Allah ya halicce su kuma ya hore musu, ba su da wani abu na al’amari kokadan, basa nuni akan fargaba ko rashi lafiya ko mutuwa ko kuma rayuwa, kawai abin sani dukkanin wadannan ayyukan shaidanune wadanda suke satar maganar mala’iku.
Wannan shine takaitaccen bayani a fasali na farko. Yanzu kuma zamuyi bayani akan fasali na biyu Insha Allah*Fasali na biyu:* Sihiri Da Bokanci Da Kuma Duba.
Dukkanin wadannan al’amura ayyukane na shaidau da aka haramta, suna ruguzawa mutum Imani ko kuma su rage masa imani, domin ba’a yin su sai da abubuwa na shirka da Allah.
1. Sihiri: Wani abune da yake a boye, kuma ba kasafe ake gane sababinsa ba, an kirashi da sunan sihirine domin anayinshi ne da boyayyun abubuwa wadanne dakyar ido yake ganinsu, sune kuma kamar layu tofi da wasu surakatai da magunguna da hayaki. Sannan shi asiri yana da hakika, domin daga cikinshi akwai wanda yake tasiri a zukata wani kuma a jiki sai ya sanya rashin lafiya ko ma ya yi kisa wani kuma y araba tsakanin miji da mata, tasirin nasa ya na kasancewa da kaddarar Ubangiji, -aikine na shaidan kuma mafi yawa ba’a kaiwa ga aikata shi sai an hada da shirka da neman kusanci ga shaidanu na abinda suke so, da kuma amfani da abinda suke so din na shirka da Allah, saboda wannan ne shari’a ta hada shi da shirka inda Annabi ( ya ce: “Ku nisanci abubuwa guda bakwai masu halakarwa”, sai sahabbai suka ce mene ne su? Sai ya ce : Shirka da Allah da kuma asiri”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito hadisin.*Sihiri yana shiga shirka ta bangarori biyu:*
Bangare Na Farko: Yadda ake amfani da shaidanu acikinshi da kuma yadda ake dogaro da su, sannan kuma ga yadda ake neman kusancin su na abinda suke so, domin su tashi tsaye su yi hidima ga mai yin asirin, kuma shi sihiri yana cikin abinda shaidanu suke koyarwa, Allah madaukakin sarki yana cewa: *“SAIDAI SHAIDANU SU NE SUKA KAFIRTA, SUNA KOYAWA MUTANE ASIRI”.* Suratul Bakarah, aya ta:102.
Bangare Na Biyu: Abinda ke cikin shin a da’awar sanin ilimin gaibi, kuma da’awar sanin ilimin gaibi tarayyane da Allah madaukakin sarki, wannan ko tsattsar kafircine da kuma bata, Allah yana cewa: *“KUMA HAKIKA SUN SANI GA DUKKAN WANDA YA ZABE SHI (ASIRIN) BA SHI DA WANI RABO A LAHIRA”.* Suratul Bakarah, aya ta:102.
Ma’ana ba shi da wani kaso, tunda ko ya kasance hakane to babu wata shakka akan cewar sihiri kafirci ne kuma shirkane yana warware akidar musulmi, kuma yana zama wajibi a kashe duk wanda yake aikata shi, kamar yadda da yawa cikin manya manyan Sahabbai suka kashe, hakika kuma mutane sun yi sanyi kan abinda ya shafi masihirci da kuma sihirin, harma sukan lissafa shi wannan wani fannine na fannoni da ake alfahari da shi har ma ake baba kyaututtuka domin zaburar da masu aikata hakan, ka ga ana hada kulab kulab da tarurruka da musabaka ta masihirta, ka ga dubundubatar mutane da ‘yan kallo duk sun halarta, lalle wannan yana nuna jahiltar wannan addini na musulunci da kuma ko’in-kula da abinda ya shafi akidah da kuma daukar mataki akan masu wada da ita.2. Bokanci Da Kuma Duba: su ne kuma masu da’awar sanin gaibu da abubuwan da suke na gaibi, kamar labarikan abunda zai faru nan gaba a kasa, da abunda ake saran zai faru, kuma inane wurin abin nan da ba’a gani ba, suna yin wannan ne ta hanyar anfani da shaidanu wadanda suke sato Magana daga sama, Allah madaukakin sarki yana ce wa: *"SHIN IN BA KU LABARIN WADANDA SHEDANU SUKE SAUKA A WURIN SU? SUNA SAUKA NE AKAN DUKKAN TINTIRIN MAKARYACE KUMA MAI LAIFI. SUNA JEFA MAGANA MAFIYAWANSU KARYA SUKE YI”.* Suratus Shu’ara’i, aya ta: 221-223.
Domin shi shaidani yana sato kalma guda daga cikin maganganun mala’iku, sai ya jefa wannan maganar a kunnuwan bokaye, sai shi boka ya kirkiri karaya guda dari sai ya hada da wannan Kalmar da shedan ya jefa masa, sai mutane su dinga gasgata shi ta sanadiyyar wannan Kalmar da ya ji ta daga sama.
Allah shi kadai ne ya kebantu da sanin gaibi, duk kuma wanda da’awar ta rayya da shi a wani abu guda cikin wadannan abubuwa ta hanyar bokanci ne ko ma ta wata hanyar ko ya gasgata wanda ya yi da’awar hakan to hakika ya sanyawa Allah tarayya a abinda yake ya kebanci Allah ne shi kadai. Shi bokanci baya taba rabuwa da shirka, domin neman kusanci ne da shedanu da abinda su shedanun suke so, wannan ko shirkace a Rububiyyah ta yadda da’awar tarayya da Allah ne a iliminsa, kuma shirkace a Uluhiyyah ta hanyar neman kusanci ga wanin Allah da wani abu da ake bautawa Allah da shi.An karbo daga Abuhurairata daga Annabi: “Dukkan wanda ya je wurin boka ya kuma gasgatashi abinda ya fada, tho hakika ya kafirta da abinda aka saukarwa Annabi Muhammad s.a.w”. Trimizi da Abudawuda ne suka ruwaito.
Yana daga cikin abinda ya zama wajibi a fadakar akansa kuma a fadaku da shi: Cewar lalle masihirta da bokaye da masu duba, suna matukar wasa da tauhidin mutane, ta yadda suke bayyana kamar masu magani, sai su umarci mara lafiya da ya yi yanka ga wanin Allah, kamar ya yanka rago mai siffa kaza da kaza, ko ya yanka kaza, ko kuma su rubuta musu wadansu kuraman bakake (Dalsami) wadanda suke na shirka ne da wasu surakatai na shedanu wai don neman tsari da cewa ai hirzi ne, sais u rayata a wuyansu ko su ajiye a akwatinan su ko kuma su sanya a dakunansu.
Wani kuma yana bayyana ne da sunan mai bada labarin gaibu, da bada labarin wasu abubuwan da ba’a san inda suke ba, ta yadda jahilai za su zo musu suna tambayarsu dangane da wasu abubuwan su da suka bata, sai su ba su labarinsu, ko kuma ma su kawo musu wadannan abubuwa ta hanyar ma’aikatansa cikin shaidanu.
Wasu kuma suna bayyana ne da sunan waliyyai, wanda yake da wadansu abubuwa da suka sabawa al’ada da karamomi, kamar shiga wuta kuma ba za ta yi masa komai ba, ko yanka wuka a jikinsa (Kufegere), ko kuma ya sanya kansa karkashin tayar mota kuma babu wani abu da zai faru, ko dai makamantan haka cikin ayyukan masu dabo, wacce a hakikaninta sihiri ne daga cikin ayyukan shaidanu, ya ke kasancewa a hannun waddanan nan domin su fitini al’umma, ko kuma kawai wadansu al’amurane na masu rufa ido, kwatakwata ma ba su da wata hakika, kawai wadansu suddabaru ne da suke yin su a gaban masu kallonsu kamar ayyukan masihirtan fir’auna da suka yi da igiyoyi da kuma sanduna.Shehul Islma Ibnu Taimiyah yana cewa a mukabalar da suka yi masahirtan Badahi’iyyah wadanda suke bin darikar Rufa’iyyah, sai babban shehun badahi’iyya din ya ce bayan ya daga muryarsa: Mu muna da wadansu halaye, iri kaza da kaza, ya yi da’awar abubuwa na daban kamar wuta da waninta da kuma yadda sauka kebanta da wutar, kuma su suna cancantar su sallamawar wutar halin da suke ciki domin ita karan kanta wutar. Sai Shehul Islam Ibnu Taimiyah ya ce: Sai nace kuma na daga muryata cikin fushi: “Ni a yanzunnan ina kalubalantar dukkan wani mai bin darikar Rufa’iyyah a gabashin duniya yake ko a yammacinta, duk wani abu da suka yi a wuta to ni ma zan yi irin abinda suka yi dukkan wanda ya kone to an yi Nasara a kansa, a wanilokacin kuma ya ce: To tsinuwar Allah ta tabbata a kansa, amma hakan bayan an wanke jikin mu da Khal da kuma ruwan zafi, tho sai sarakuna da sauran mutane suka tambayeni akan wannan sharadi sai na ce: domin suna da wadansu dabaru wurin shiga wuta, suna yin wadansu abubuwa kamar manshafawa da kwadi da kuma Narinj da kuma dutsan dalk, sai mutane suka fashe da ihu, sai (shi shehun darikar) kawai ya fara bayyanar da ikonsa, sai ya ce: Ni da kai mu je mu lulluba a wata bariya bayan an shafe jikin mu da farar kasa, sai na ce: tashi mu je (in ji Ibnu Taimiya) sai naita maimaita masa akan ya tashi mu ke mu yi hakan, sai ya meke hannu zai cire rigarsa, sai na ce: A’a, har sai ka wanke jikinka da ruwan zafi da kuma Khal, sai kawai ya rikice akan irin al’adarsu sai ya ce: Dukkan wanda ya kasance yanakaunar sarki to ya kawo itatuwa, ko kuma cewa ya yi: ya kawo dauri dauri na itatuwa, sai na ce (in ji Ibnu Taimiyah) wannan wata doguwar Maganace da kuma raba kan mutane, ba wai shine abin nufi ba, kawai a kunna kyandir in sanya yatsa n aka sanya yatsanka bayan an wanke, duk kuma wanda yatsan shi ya kone to tsinuwar Allah ta hau kanshi ko kuma an yi Nasara akan shi, to fa lokacin da na fadi haka sai ya rikice ya kaskanta’’. nan maganar ta kare, majmu’ul fatawah, juzu’i na 11, shafi na: 445-446.
Babban abin nufi dai shine wadannan shedanun suna yiwa mutane karya ta hanyar irin wadannan boyayyun dabarun.