MU SAN AZUMI A SHARI'ANCE 10

_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(10)

HUKUNCIN MAI AZUMIN DA YA CI ABINCI DA MANTUWA!!!

Idan mutum yana Azumi sai ya ci ko ya sha abin sha da mantuwa, azuminsa ingantacce ne, babu ramuwa a gare shi bare kaffara.

عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ نَسِىَ وَهُو صَائِمٌ فَأَكَلَ أَوْ شَرَبَ فَلْيَتِمَّ صَوْمَهُ فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ الله وَسَقَاهُ." (رواه البخارى)

An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda ya manta ya ci ko ya sha lokacin da yake Azumi, to, ya ci gaba da azuminsa, hakika, Allah ne ya ci da shi ya shayar da shi.” (Bukhari ne ya rawaito)

Idan mutum yana Azumi sai amai ya zo masa ya amayar to, babu komai a gare shi.
Don fadin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce: 
“Wanda amai ya zo masa (lokacin yana Azumi) ya amayar ba komai a gare shi, idan kuwa da gangan ya jawo aman to, ya rama Azumi.” (Tirmizi ne ya rawaito).

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Post a Comment (0)