*Tambaya:*
Assalamu alaikum
Mlm barka da yau dafatan Allah ya albarkaci rayuwarka data iyalanka baki daya.
Tambayata itace shin wadanne wurare ne Addinin musulunci yayi hani akan kada ayi sallah a wurin. ❓
Nidai natabaji wani mlmi yace harda makabarta.
Jazakumullahu khairan 🙏
.
*Amsa:*
Waalaiku mussalam.
Babu shakka manzon Allah saw ya fada cikin hadisin da Abdullahi bn Umar ya rawaito cewa:
*"أن رسول الله صلى الله عليه وسلم نهى أن يصلى فى سبعة مواطن فى المزبلة والمجزرة والمقبرة وقارعة الطريق وفى الحمام وفى معاطن الإبل وفوق ظهر بيت الله“*
الترمذى (٢٧٩)
*"Lallai manzon Allah saw ya hana a yi sallah a wurare guda bakwai: a bola, a kwaataa (mayankan dabbobi), a makabarta, a tsakiyar hanya, a bayin wanka, a garken raquma, a saman ďakin Allah (Ka'aba)”* Imam Tirmizi 279.
والله أعلم.
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
*🕌Islamic Post WhatsApp.*