MU SAN AZUMI A SHARI'ANCE 13


_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(13)

*DAREN LAILATUL KADARI*

Ya zo a cikin Hadisi, ana samun Daren Lailatul Kadari a kwanakin mara na goman karshe na watan Azumi a daren ashirin da daya ko ashirin da uku ko ashirin da biyar ko ashirin da bakwai ko ashirin da tara da dare na karshen watan Ramadan.

Nana Aisha (R.A) 
ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: 
“Ku nemi Daren Lailatul Kadari a goman karshe.”
 (Bukhari ne ya rawaito).

Ana so a yawaita addu’a a Daren Lailatul Kadari. 
Nana Aisha (R.A) ta ce, na tambayi Manzon Allah (S.A.W)
Na ce, ya Rasulullahi, idan na ga Daren Lailatul Kadari me zan fada a cikinsa? Sai Manzon Allah (S.A.W) 
ya ce, ki ce: 

*"اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى."*

“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa’afu anni.”
Ma’ana:

 “Ya Ubangiji, hakika, Kai mai afuwa ne, kuma kana kaunar yin afuwa, 
ya Allah ka yi min afuwa.” 
(Bukhari da Muslim ne suka rawaito).

Kuma ana so a karanta wadannan ayoyi masu yawan lada.
1- آيَةُ الْكُرْسِيُّ 
2- آمَنَ الرَّسُولُ 
3- إِذَا ذُلْزِلَتِ اْلأَرْضُ 
4- قُلْ يَأَيُّهَا الْكَافِرُونَ
 5- قُلْ هُوَ الله أَحَدٌ
 6- سُورَةُ يَاسِين.


1. Ayatal Kursiyyu 
2. Amanar-Rasulu 
3. Izazul zilatul ardu 4. Kulya ayyuhal kafiruna 
5. Kul huwallahu ahad 
6. Suratu Yasin.

Kuma a yawaita istigfari, tasbihi, salati ga Annabi, sannan a roki alhairan duniya da na lahira.

Alhamdulillah Nan muka kawo karshen wan nan darasi mai Albarka,

Muna rokon Allah yasa Albarka acikin abinda muka karanta kuma yabamu ikon yin aiki da shi , San yakarbi ayyukan mu na kwarai yakuma amsa Addu'oin mu

Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)