SHIN KANA SON LADAR AZUMI DA SALLAR DARE?

KANA SON LADAN AZUMI DA SALLAN DARE NA SHEKARU MASU YAWA A CIKIN MINTUNA?? 

Sahabi Ausu bin Ausi Allah ya kara masa yarda yace: Naji manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana cewa "Duk Wanda yayi wanka ranan juma'a sannn ya tafi da wurwuri, ya tafi da kafa bai hau abun hawa ba, ya zauna kusa da liman, ya saurari khudba batare da yayi lagawu ba, ya kasance zai samu ladan aikin shekara guda azumin cikinta da sallan darenta, abisa kowane taku yayi na tafiya masallcin".
سنن أبي داود ٣٤٥

Ya Allah, yi ta'ammuli ya kai dan uwa mai daraja game da wannan bonan za da Allah ya bawa bayinsa, taku guda daya yana dai dai da azumi da sallan kwana 365, taku nawa zaka yi kafin isa masallaci?? Gwada lissafa takun da zaka yi kafin ka isa, sai kayi multiplying by 365 abunda ya baka shine gwargwadon kwanakin da za'a baka ladan azuminsu da sallolinsu. 
     Sai yasa wasu malamai suke cewa babu wani hadisi na manzon Allah da yafi wannan ambaton lada mai yawa. An ruwaito cewa Sa'eed bin Musayyib yana cewa "Zuwa sallan juma'a da wuri shi yafi soyuwa agareni akan zuwa aikin hajjin nafila".
    Kada ka manta ya kai dan uwa, Abubuwa biyar kawai zaka yi kasamu wannan garabasa, gasu kamar haka; 
1. Wanka
2. Zuwa masallaci da wuri
3. Tafiya da kafa
4. Matsawa kusada liman
5. Yin shiru da kuma sauraron khudba. 
    Allah yasa mudace. 

# ZaurenFisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)