KANA SON TSARI?

KANA SON TSARI, LIZIMCI......!!! 

Sahabi Abi huraira ya ruwaito hadisi cewa wani mutumi yazo wurin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana koka irin azaba da yasha alokacin da wata kunama ta harbeshi adaren jiya, sai Manzon Allah yace masa "Amma dai lokacin da kayi yammaci baka ce A'UDHU BIKALIMAATILLAHIT TAAMMAATI MIN SHARRI MA KHALAQA ba, ai da bazata iya cutar dakai ba"
مسلم ٢٧٠٩

Imam Al-Manawy Allah ya masa rahama yana cewa "Idan mutum ya fadi wannan Kalmar tare da karfin yaqeeni da kuma yarda da Allah, to wallah kamar yadda Manzon Allah ya fadane babu abunda zai cutar dashi daga cikin halittu dama dama wasunsu har ya bar wurin da ya fadi addu'ar acikinsa. 
      Imam Al-Qurdubi Allah ya masa rahama yake cewa "labari ingantacce, zance kuma na gaskiya, wallah tunda najishi nake aiki dashi kuma wani abu bai taba cutar dani ba, har sai watarana awani dare da ban karantaba, sai kunama ta harbeni" 
فيض القدير ١/٤٤٦

Note:
Ana karanta wa sau uku da yamma. 

# Zaurenfisabilillah 
https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)