TAMBAYA TA 017


*ZAN IYA TAFIYA SUJJADA DA GUIWA KO KUMA DOLE SAI DA HANNU ?*


*Tambaya*
Assalam Alaikum.
Mallam, dangane da zuwa sujada, tafiya da gwuiwa ko da hannu a cikin sallah, wanne yafi inganci?

*Amsa*
Wa alaikum assalam
Kowanne mutum zai iya yi, saboda akwai riwayoyin hadisi mabanbanta akan haka, kuma kowacce riwaya akwai malaman Hadisin da suka ingantata.

Abin da ya fi kamar yadda Malaminmu Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim ya fada mana a karatunsa na SunanutTirmizi shi ne: wani lokocin mutum ya tafi da guiwa, wasu lokutan kuma da hannu, saboda aiki da riwayoyin gaba daya, da kuma fita daga sabanin Malamai.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*
04/03/2020

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)