TAMBAYA TA 019

*MATSAYIN AURE IDAN MIJI YACE DA MATAR SA BAKI DA HAKKI A KAINA !*


*Tambaya*

Assalamu alaikum malam munsami sabani da mijina sai yace bashida hakki akaina ya ya aurenmu yake Nagode


*Amsa*

Wa'alaykumussalam
Kalmar bakida hakki akan mijin ki bata nuna saki, sai inya tabbar da cewa shi saki yake nufi..
Domin da'awar kore hakki tsakanin ma'aurata da'awace 'kazibah' wato da'awar karya domin dukkan ma'aurata kowa yasan yana da hakki akan juna.
Bacin rai kan sa miji furta ire iren wadan nan kalaman musamman ma gashi kince kun samu sabani wanda ke nuna kalmar nada alaka da irin sabanin da kuka samu.
Don haka dai auren ku na nan, saifa in mijin ya nuna saki yake nufi ko kuma ya furta saki karara.

Sai a kiyaye dukkan abinda zai yanyo furta irin wadannan kalaman. 

Wallahu A'alam

Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)

19/02/2020

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)