HIKAYAR ATTAJIRI DA MACIJIYA DA KUMA ABU-IRSI


LABARIN ATTAJIRI DA MACIJIYA DA KUMA ABU-IRSI

(Qissa ce ta tarbiyya domin yara Qanana)

Wata rana wasu ayarin ‘yan kasuwa suka fita domin fatauci zuwa birnin Basrah kudancin Iraqi, can suna cikin tafiya a kan hanyarsu sai suka zo wani dausayi mai koramu da ciyayi masu duhu da kuma wurin wanka da hutawa, to daman iskar da ake yi a wannan lokaci zafi gareta, samun wannan wuri ke da wuya sai wadannan ‘yan kasuwa suka sauka domin su huta su biya wasu bukatun nasu kadan.

Sai daya daga cikinsu ya nufi wurin wata duhuwa ta ganyen da ke fitowa gefen karama inda suke sarke da juna suka hadu suka bada wani yanayi na tanti (dan karamin dakin tafi-da-gidanka), nan take ya shige ciki ya boyewa zafin rana, to saboda sanyin ciki sai ya fara jin gyangyadi yana kama shi, sai kawai ya mike kafa ya kama bacci! Su kuwa abokan tafiyarsa basu san abokinsu yana cikin rumfar ganyayyaki ba yana bacci, ko da suka gama abinda suke sai suka tashi suka daura kaya suka hau rakumansu suka yi gaba zuwa birnin Basrah.

Bayan wasu awanni sai wannan dan kasuwa ya farka daga baccinsa, a tsammanisa wannan ayari suna nan a wurin da suka sauka suna hutawa, sai ya yunqura da nufin ya fita daga cikin wannan tanti na ganye, ai kwatsam sai ga macijiya ta fasa kai a bakin raminta, tun da yake bai taba ganin macijiya mai girmanta ba!

Ko da wannan mutum ya ga macijiyar nan ba zato ba tsammani sai ya ji tsoron tsallakawa ta inda ta tsare masa hanyar fita gashi kuma yanayin sarkakiyar bishiyoyin ba zai yiwu ba ya fita ta wani wuri in banda ta inda ya shiga, ya kama ambaton Allah tare da rokonsa gami da yin tawassuli da soyayyar Annabi (SAW).

Ai yana cikin wannan hali sai kawai ya ga wata dabba mai kama da dila saidai bata kai girman dila ba ana kiranta (Ibnu Irsi), kowa ya san wannan dabba kuwa tana cikin manyan abokan gabar macizai, ai ko da (Ibnu Irsi) ya ga macijiya sai ya tsaya yana kallonta yana nazarin yadda zai yi mata ya kama ta, jim kadan sai ya juya ya koma inda ya fito.

Bacewarsa ke da wuya sai gashi ya dawo tare da dan'uwansa (suka zama biyu) daya ya tsaya daga bangaren dama na kofar tanti, daya kuma ya koma daga bangaren hagu, don haka sai suka kasance daya a wajen kan macijiya dayan kuma a wajen jelarsa, ita kuma macijiyar nan duk bata kula da su ba, (ita dai hankalinta yana kan mutumin nan), duk wannan abu da ake yi mutumin nan yana kallon abin mamaki tare da firgici da idanuwansa!

Lokaci daya suka yi mata dirar mikiya a tare, sai ga kan macijiya a bakin (Ibnu Irsi) jelarta kuma a bakin dayan! Macijiya ta yi yunkurin da duk za ta iya amma bata samu damar guduwa ba, daga nan suka ja ta nesa inda babu wanda zai zo wucewa ya gansu, ko da ganin haka sai wannan tajiri ya fito daga tantin da yake, ya na godiya ga Allah da ya kwace shi daga wannan musibah.

📍📍📍
*WASU DAGA FA’IDOJIN WANNAN QISSA GA YARA:*
▪1. Lalle addu’a makamin mumini ce
▪2. Muhimmancin addu’a a yayin da ka sauka a sabon wuri irin wadda shari'ar Musulunci ta karantar. (a duba littafin Hisnul Muslim) sai a koyawa yara.
▪3. A tare da kowane tsanani akwai sauki.
▪4. Bibiyar halin da dan’uwanka ya ke ciki yana da matukar muhimmanci, domin hakan zai taimaka har ka san irin halin da yake ciki. 

Fassara:
M. Jamilu Nakumbo
16/2/2018

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)