ZUNUBIN DA ALLAH BĀ YA YAFEWA.



ZUNUBIN DA ALLAH BĀ YA YAFEWA.

*Tambaya:*

Assalamu alaikum malam barka da warhaka malam Dan ALLAH wane zunubine mafi Muni Wanda in mutum ya aikatashi ALLAH bazai yafe mashiba ALLAH ya baka ikon ansaman tambayata ngd
.

*Amsa:*

Wa'alaikumussalamu Warahmatullah.

Zunubi mafi girma shi ne *Shirka,* wato kafirce wa Aʟʟαн(ﷻ) da bauta wa waninSa. Aʟʟαн(ﷻ) yā ce:

*”إِنَّ اللّهَ لاَ يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَن يَشَاءُ وَمَن يُشْرِكْ بِاللّهِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلاَلاً بَعِيداً“.*

Ma'ana: *“Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa.”* [Surah 04: 116].

Nassin alqur'ani da sunnah duka sun tabbatar da cewa shirka ita ce laifi mafi girma, kuma Allah bā ya gafarta wa mushirikai. 

Wallahu A'lamu.
.

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*

https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)