KIRA GA MASOYA A WATAN RAMADAN


KIRA GA MASOYA A WATAN RAMADAN.

Yi wa masoyiyarka ƙyauta da kayan shan-ruwa hakan zai ƙara janyo maka martaba da ƙarin girmamawa daga wajen ta da kuma ƴan’ uwanta.

Tabbas, wannan al’ada ce da ta shahara wajen ƙara danƙon soyayya a tsakanin saurayi da budurwa a ƙasar Hausa. Wannan ita ake kira da 'Toshin barka da shan-ruwa’.

Ke ma kuma za ki iya bawa saurayin naki kayan shan ruwa, domin samun lada da ƙaruwar soyayya a tsakani, ta hanyar faranta ransa.

Kar da ku manta ana fara aikawa da kayan shan-ruwan ne tun goma ga azumi. Ana kuma bada abubuwa ne nau’in su kayan marmari ko abubuwan sa wa a baka. Misali: 
Ayaba🍌
Gwanda🥑
Lemo🍈 
Abarba🍍 
Madara🧊 
Bambita🧃 da sauransu.

Allah ya bar soyayya har ya zuwa bayan aure amiin


@Young fillo 

Zaman lafiya shi ne muradina🙏
Post a Comment (0)