TAMBAYA TA 61

HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A
SAKETA
TAMBAYA
Assalamu alaikum Malam. Mace ce aka aurar tana
'yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai mijin yayi
tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa
aka rubuta mata saki tace ya saketa, bayan ya dawo
yace bai saketa ba, amma ba'a yarda ba. Da ta kare
idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya
kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta
samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da
tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da yaran
data haifa da miji na biyu?
AMSA:
Wa alaikum assalam Malam amsar wannan tambaya
yana da mutukar wahala, saidai na nemi taimakon
wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :
*1.* Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci
saboda ta yi aure cikin aure.
*2.* Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a
matsayin mazinaciya take, saboda haka duk
kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.
*3.* Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu,
'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a
baya.
*4.* Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba
tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har
yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.
*5.* Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare
da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta
tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma
Allah ya hana auren mazinaciya.
*6.* Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda
girman zunubin da ta aikata.
*7.* Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san
shari'ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.
Allah ne mafi sani.
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Post a Comment (0)