ABUBUWAN DA KE ƁATA AZUMI


*DAY 09* 
 ```RAMADAN ARTICLES``` 

 *ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI* 
 
Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mai Azumi ya nesance su, domin idan ya aikata su da Rana tsaka a Ramadana, Azumin sa yana ɓaci, zunuban sa su yawaita, Malamai sun gano cewa waɗannan abubuwa masu bata Azumi, za’a iya kasa su karkasuwa mai yawa, dangane da ire-iren sakamakon da ake haifarwa daga gare su kamar haka:
 
Na farko: *CI DA SHA DA GANGAN;* wannan yana bata Azumi abisa haduwar Malami.
 
Na biyu: *KAKARO AMAI DA GANGAN;* duk wanda ya fitar da wani abu daga cikin shi to Azumin shi ya baci, amma duk kuwa wanda amai ya rinjaye shi to babu komai akanshi, kuma Azumin shi yayi –in Allah yaso- dalili akan haka fadar Manzon Allah: 

 ```“Duk wanda Amai ya kubuce masa alhali kuma yana Azumi wannan babu ramuwa akanshi, amma idan ya ƙaƙaro shi da gangan to sai ya rama Azumi”```      

 _[Abu Dawuda ya ruwaito shi daga Abu Hurairah]_ 
 
Na uku: *HAILA DA NIFASI;* idan Mace tayi Haila ko tayi Nifasi (Jinin Haihuwa) a wani yanki na wuni a farkon wuni ne ko a karshen sa to anan sai taci abincin ta, sai taciyar da Miskinai sittin a kowacce Rana, idan kuwa ta cigaba da Azumi to azumin ta bai yi ba. 

#Asha_Ruwa_Lafiyah

Domin samun jerangiyar waɗannan Articles, kasance da mu a
https://t.me/annasihatvchannel
Post a Comment (0)