MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 5


_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(5)


LOKACIN FITAR DA ZAKKA:
DAKUMA SHARADAN WAJABCINTA;

 Lokacin fitar da Zakka ya danganta ne da nau’in dukiyar. Idan zakkar kudi da dabbobi, 
da kayan sayarwa ce, to sai dukiyar ta shekara, 
bayan ta kai nisabi.

 Amma idan Zakkar amfanin gona ce, 
toh ana fitar da ita ne a lokacin da aka girbe ko aka tsinke.

  Zakkar ma’adanai da ta zuma kuwa, 
a wajen mahzahar Hanafiyya, 
ita ma ana fitar da ita a yayin da aka fito da su. 

(Duba FiKhul Islami Wa Adillatahu, juz’i na 3, sh: 1814 – 15)

SHARADAN WAJIBCIN TA:

 Dangane da abin da ya gabata, za mu fahinci cewa,
 tsabar kudi da kayan sayarwa suna buKatar sharuda biyar kafin a fitar musu da Zakka,

 su ne: 
1-Musulunci, 
2-‘yanci, 
3-mallaka,
4- cikar nisabi, 
5-da cikar shekara.

 Idan kuwa Zakkar dabbobi ce, 
to, sai a Kara sharadi daya shi ne, kasancewa suna fita kiwo. Ba a daure su ke ana nemo musu abinci ba, 
(watau ba turkakku ba). 

Haka kuma idan amfanin gona ne, 
to shi ma sai a Kara sharadi daya, 
watau ya kasance abinci ne ga dan’adam. 
Amma a fitar da sharadin cikar shekara.

 (Duba Al-FiKhul Muyassar na Ahmad Isa, juz’i, 1, sh;220-222)

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248
Post a Comment (0)