ALBISHIRIN KI MAI HIJABI DA NIƘABI A LIKITANCE


ALBISHIRINKI MAI HIJABI DA NIKABI A LIKITANCE.
(BABI NA BIYU 02)

AMFANIN HIJABI A LIKITANCE:
Malaman zamani sun yi bincike sun tabbatar cewa duk inda ALLAH ya kira ta da suna al'aura kuma yace a rufe ta tafi jin tabi kuma ta fi kamuwa da cututtukar zamani, shi ya sa ALLAH ya umurci maza da su rufe al'aurar su daga cibiya zuwa guiwa, saboda waɗannan wajajen sun fi kamuwa da cuta a wajan namiji, amma mace kuma malamai suka ce tun daga gashin kanta har zuwa kasa, shi ya sa ALLAH yace ta rufe gaba ɗayan jikin ta. Kuma malaman suka kara da cewa abinda ya sa ALLAH ya bambanta halittar namiji da mace shi ne namiji ya fi yawan fita waje da yawo a rana da buɗe jiki don neman abinci, shi ya sa jikin sa ya fi jikin mace karfi ta wajen kamuwa da cuta.

Sa'annan kungiyar binciken likitoci na Birtaniya sun yi bincike sun gano cewa cutar CANCER (jeji/daji) mafi muni wanda ake kiranta da suna melanoma ta fara yaduwa sosai musamman ma a wajen yan mata kanana, bayan bincike akan haka sai suka gano cewa cutar ta fi kama matan da suke buɗe jikin su suna yawo musamman ma masu saka gajerun tufa da mini-skirt da show me your shoulder da masu saka material mai shara-shara da sauran su, sannan wannan cutar bata tsayawa a kansu ba kawai har tana wucewa ta shafi 'dan dake ciki, idan aka haifi yaro sai ya kamu da cuta, kuma suka kara da cewa dalilin wannan cutar ita ce yawan buɗe jiki ta yadda rana zai yi ta haska jikin su, kuma ita wannan cuta idan ta kama mace yana wahala likitoci su magance ta.
 Wannan yana daga cikin hikimar da ya sa addinin musulunci ya umurci mace ta rufe gabaɗayan jikin ta saboda ALLAH Yana son ta Yana kuma son kiyaye mata lafiyar ta. Kamar yadda malaman bincike na Amurka suma sun tabbatar da cewa matan da suke rufe gaba ɗayan jikin su yawanci basa kamuwa da cututtukan zamani kuma sukan kasance cikin koshin lafiya.

Sa'annan wata likita mai suna duktura mai assmahi malama daga jami'ar ainush'shams a layin Abbasiyya a birnin Al'kahira na kasar Misra(Masar) tace Hijabi yana kare gashin kai ta yadda bazai karye ya fadi ba domin shi gashi yana samun abincin sa ne a jikin mutum, dan haka duk lokacin da mace take barin gashin ta a buɗe ya dade rana yana dukan sa kuma iska tana busar da shi to gashi bazai yi yawa ba sai dai ya dinga karyewa.

Sa'annan akwai wani babban farfesa mai suna Malker mutumin Canada (Kanada) wanda shi ba musulmi bane yana aiki a cibiyar bincike ta Jiddah a Sa'udiyya ya yi bincike a game da wata cuta da take kama mata sai ya gano cewa duk duniya ba inda yake da ƙarancin masu kamuwa da irin wannan cutar kamar matan Sa'udiyya, sai ya sake maimaita binciken sa a kan sauran garuruwan da suke makwabtaka da Sa'udiyya ko yana ganin cewa garin nasu ne babu cutar, sai ya ga dai ba haka bane, dalilin da yasa matan Sa'udiyya suke da ƙarancin wannan cutar kadai shine rufe jikin su gabaɗaya dasukeyi ta yadda rana baya dukan su da wuri kuma iska bata dukan jikin su sosai, kuma ita wannan cutar dama ana samunta ne daga hasken rana dakuma zafinta. Kunga wannan mutumin arne ne amma ya tabbatar da cewa rufe jiki gabadaya yana kare mace daga cututtukar zamani. Shi yasa akeso musulmi ya rinka sallamawa dakuma bin tsarin musulunci koda baisan hikimar abun ba, domin Allaah da ManzonSa Baza su yi umurni da abunda babu hikima da alfanu ga ďan Adam a addininsa da rayuwarsa ba. 

Allaah Ya kara tabbatar damu akan addinin musulunci tareda bin umurnin Allaah sau-da-'kafa.

Rubutawa: Abu Albaniy Al- Athariy.
Post a Comment (0)