*IDAN ZINA TA YI YAWA A CIKIN AL'UMA, CORONA ZA TA SAMU GINDIN ZAMA !*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, Mal. Wani bawan Allah ne yayi sabon aure bayan kwana ashirin sai ya gano matar nada ciki sai ya tambaye ta tsakaninta da Allah, sai ta ce cikin ba na shi ba ne, amma kuma shi ma wanda ya mata cikin sau daya ya yaudareta ya taba tarayyya da ita, shi ne take cewa ya rufa mata asiri a zubar da cikin, Shi ne yake neman mafita da shawara.
*Amsa*
Wa alaikum assalam to dan'uwa akwai hukunce-hukunce Kamar haka:
1. Tun da ba cikinsa ba ne, kamar yadda ta tabbatar ya wajaba ya dakata da saduwa da ita, Annabi (SAW) yana cewa; "Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar wani.
*2.* In ya tabbata fyade aka mata, za'a iya zubar da cikin mutukar bai wuce wata daya ba, tun da ba'a busa masa rai ba, kuma ba'a za'a tashe shi ranar Alkiyama ba.
*3.* A Mazhabar Malikiyya auransu Bai Yi ba, saboda ya aure ta cikin idda.
*4.* Mutukar ba su kai ga Alkali ba, ya hallata ya suturtata kamar yadda tarin hadisai su ka yi umarni da haka !!.
*5.* Ina yiwa Al'uma nasiha da tsoran Allah, saboda zina ta yawaita a cikinmu, wannan yasa babu Mamaki Annobar Corona ta dabaibaye mu.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
1/05/2020
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*