ALHAJI DA HAJIYA


Alhaji da Hajiya
Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gida a wani gari, akwai alhaji da hajiya a gidan, kuma akwai wani É“arawo yana da sunaye da yawa, sai ya je gurin mai gadin gidan. Da mai gadi ya gan shi sai ya tambaye shi sunansa, sai É“arawo ya ce sunansa salati, sai mai gadi ya tambaye shi gurin wanda ya zo, sai ya ce gurin alhaji ya zo, sai ya ce da shi ya wuce.

Da É“arawo ya shiga gurin alhaji sai alhaji ya tambaye shi gurin wanda ya zo, sai ya ce gurin hajiya ya zo. Sai alhaji ya tambaye shi sunansa, sai É“arawo ya ce sunansa Alanta, sai alhaji ya ce da shi ya wuce. Daga nan kuma sai ya wuce gurin hajiya. Da ya isa gurin hajiya sai ta tambaye shi sunansa, sai ya ce da ita sunansa dambu, sai ta ce da shi gurin wa ka zo? Sai ya ce da ita gurinki na zo, sai ta ce da shi “me ka zo yi”, sai ya ce “sarÆ™ar wuyanki zan sace”. Sai ya shaÆ™e mata wuya zai Æ™wace sarÆ™ar, sai ita kuma ta fara kururuwa tana cewa, “alhaji dambu ya shaÆ™e ni”. Sai alhaji ya ce da ita “kora da ruwa”, har sai da É“arawon nan ya cire sarÆ™ar gwal É—in da ke wuyan hajiya ya fita.

Bayan fitarsa sai alhaji ya shiga gurin hajiya, sai ta gaya masa abin da ya faru. Sai alhaji ya fito waje da sauri yana kururuwa yana cewa “Mai gadi kama Alanta”. Sai shi kuma mai gadi ya fara taka rawar alanta. Da alhaji ya iso wajen mai gadi ya gaya masa abin da ya faru, sai mai gadi ya fito waje da gudu yana kururuwa yana cewa “Jama’a ku kama salati”, sai mutanen gari suka fara salati.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya
Post a Comment (0)