JATAU DA MUTUWA


JATAU DA MUTUWA
Wai wata rana Mutuwa ta zo wa Jatau tace masa lokacinka yayi, sai Jatau yace gashi kuwa ban shirya ba, Mutuwa tace ko baka shirya ba lallai yau tafiya zaka yi, don sunanka ne na farko a saman takardata, jatau yayi rarrashin duniya akan mutuwa ta kyaleshi mutuwa taki.

Da ya fahimci mutuwar ba zata kyaleshi ba sai dabara ta fado masa sai yace wa mutuwa to me zai hana ki bari in dan kawo maki abinci ki ci kafin mu tafi? Mutuwa ta zauna Jatau ya tafi kawo mata abinci.

Da yaje wurin dauko abincin sai yasa maganin bacci cikin abincin ya kawo wa mutuwa, da mutuwa ta ci abincin sai ta kama bacci, da jatau yaga tayi bacci sai ya dauko takardar da sunayen mutane suke sai ya goge sunansa daga saman takardar ya rubuta a kasan takardar.

Da mutuwa ta farka daga bacci sai tace wa jatau saboda jin dadin karramawarda kayi mini da kuma dadin abincinka da naji har nayi bacci, ba zan fara sunayen mutane daga saman takardar ba zan faro daga kasan takardar. Jin haka sai Jatau ya fadi sumamme.

Darasi

Don haka yan uwa kun ga dai ko a cikin tatsuniya babu mai iya canja lokacin mutuwarsa, idan lokaci ya yi to dole ne a amsa kira, ko ka shirya ko ba ka shirya ba. Don haka ko da yaushe mu zama cikin shiri kada mutuwa ta riske mu ba mu shirya ba.

Allah ya sa mu cika da imani
Post a Comment (0)