AYYUKA MASU SAUƘI AMMA SUNA DAIDAI DA AIKIN HAJJI DA UMURA

AYYUKA MASU SAUƘI AMMA SUNA DAIDAI DA LADAN HAJJI DA UMRAH.

1- Ɗabaraaniy da Haakim sun ruwaito hadisi da isnadinsu zuwa ga sahabi Anas bn Malik yace: Manzon Allaah(s.a.w) Yace: (Duk wanda yayi sallar Asubah a cikin jam'i, sannan ya zauna ya cigaba da zikiri (misali: Azkãr na bayan sallar asubah, karatun Qur'ani, da makamantansu) har zuwa rana ta fito ba tareda alolanshi ta karye ba, sannan ya tashi yayi sallah raka'a biyu, Allaah Zai bashi ladan Hajji da Umrah). (Sahihut-Targheeb:'86').

2- Tirmizhiy ya ruwaito hadisi da isnadinsa zuwa ga sahabi Abū Umãmatal- Bãhiliy yace: Manzon Allaah(s.a.w) Yace: (Duk wanda yayi sammako zuwa masallaci babu abunda ya kaishi sai koyan wani abu na alkhairi ko saninshi; Allaah Zai bashi ladan Hajji da Umrah). (Sahih wa Da'if Sunanut-Tirmizhiy:586).

Sai dai hakan baya hukunta faralancin Hajji ko Umra ya sauka daga kan mutum, abunda akeson bayyanawa shine wadannan ayyukan ladansu daidai yake da ladan Hajji da Umrah.

ALLAAH YA BAMU IKON AIKATA SU DA KUMA LIZIMTAR SU

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
28/November, 2015.

Post a Comment (0)