BIDI'O'IN DA AKE YI DANGANE DA KARANTA ALƘUR'ANI


BID'O'I DA KURA-KURAI DA AKE YI DANGANE DA KARANTA QUR'ANI.

A jiya ne muka kawo falaloli da darajoji na makaranta da mahaddata Qur'ani, amma wani hanzari ba gudu ba; waɗannan darajoji da falaloli bazasu tabbata ba sai an nisanci kura-kurai da bid'o'in da wasu suka ƙirƙira suka jinginawa Qur'anin ko kuma yadda ake karantashi.
  Amma kafin nan, ga wasu daga cikin ƙa'idoji da hanyoyin da malamai suka bayyana yadda ake gano bid'ah a musulunci:
1- Canza siffa ko yadda Manzon Allaah ya karantar.
2- Ƙari ko ragi abisa yadda Manzon Allaah ya karantar.
3- Keɓance wani wuri ko lokaci wanda bai tabbata a shar'ance ba.
4- Ƙirƙirar wata ibadah saboda wasu dalilai da basu tabbata a shar'ance ba.
5- Ƙirƙiro wata ibada wadda gabaɗaya ba ta da asali a musulunci, musamman tare da ƙudurce samun lada akanta. d.s.

  Sannan ma'anar bid'ah shine duk wani abu da aka ƙirƙira aka jinginawa shari'ah, wadda a zahiri tayi kama da shari'ar! amma ba shari'ah bace, musamman idan aka kudurce samun lada akanta.

  Daga cikin bid'o'i da kura - kurai da akeyi wurin karanta Qur'ani sun hada da:
1- Lizimtar fadin (sadaqallaahul-azheem) a ƙarshen karatu.
2- Tangīmi, ko wuce iyaka a cikin hukunce-hukuncen tajwidi, musamman maddoji da gunnoni da haruffa.
3- Keɓance karatun suratu Yãsīn da nufin biyan buƙata.
4- Haɗe ayoyi biyu ko fiye da haka da numfashi ɗaya; koda kuwa suna da alaƙa da juna.
5- Barin jan wasu maddoji da nufin ai ba dole bane.
6- Rera Qur'ani kamar yadda ake rera waƙa.
7- Ƙoƙarin kwaikwayon muryar wani makaranci na musamman ƙarfi-da-yaji.
8- Karatun Qur'ani ana rangaji ko kuma rashin nutsuwa yayin karantashi.
9- Haɗa ƙira'o'i ko riwayoyi fiye da ɗaya a lokaci ɗaya cikin sallah ko wajen ta.
10- Karanta Qur'ani da ƙira'o'i ko riwayoyin da ba mutawatirai ba.
11- Karanta suratul Muddatthir da Muzzammil a daren da aka haifi Manzon Allaah(saw) a sallar Isha'i da Asubah.
12- Karanta surar da akwai sunan Annabi Musa a cikinta a sallar Asubah na safiyar ranar Ashura.
13- Karatun Qur'ani a wurin da ake surutu ko hayaniya.
14- Karanta Qur'ani a sanda mutum ke shan taba ko aikata wani saɓo.
15- Karanta Qur'ani a maƙabarta ko a sanda ake yiwa mamaci wanka ko sanda za a kaishi maƙabarta.
16- Faɗin "Allaah! Allaah!! Allaah!!! a sanda wani ke karatu.
17- Yin kabar-bari a ƙarshen suratul Dwuhaa zuwa suratun Naas.
18- Rera addu'ar ƙunuti ko wata addu'a kamar yadda ake karanta Qur'ani.
19- Karanta addu'a na Khatmul-Qur'an a cikin sallah ko a wajen ta.
20- Karanta suratul Fātihah da wasu surori na musamman don biyan buƙata, ba tare da yin tawassuli dasu ba.
21- Faɗin kalmar(AL- FAATIHAH) a ƙarshen suratul Fātihah.
22- Cewa (Ãammēn) a ƙarshen Fātihah, sai dai mustahabbi ne idan a cikin sallah ne.
23- Ƙoƙarin karanta wasu surori ko ayoyi da suka dace da huɗubar da akayi ranar Juma'a ko Idi ko makamantan su.
24- Sauke Qur'ani ƙasa da kwana uku.
25- Keɓance wasu lokuta ko wuri domin saukar Qur'ani.
26- Karanta Qur'ani kawai domin samun wani abu na duniya.
27- Yin azumi ko wata ibadah ta musamman a ranar sauka.
28- Sanya ko ɗora hannaye a kunni a yayin karanta Qur'ani kamar mai kiran sallah.

  Kuma malamai sun yi bayanin haɗurran da mai aikata waɗannan bid'o'i da kura-kurai zai iya faɗawa, dogaro da nassoshin da suka bayyana haka, daga cikin waɗannan haɗurra sun haɗa da:
1- Zai rasa ladar da Allaah SWT Ya tanadarwa makarancin Al- Qur'ani.
2- Yana ƙoƙarin shar'anta abunda Allaah bai shar'anta ba.
3- Yana nunawa waɗanda ba su sani ba cewa abunda yake yi dai-dai ne.
4- Sannan yana ƙoƙarin cin gyaran Allaah SWT; wanda wannan shi yafi komai haɗari.
5- Sannan a ƙarshe mutum zai tashi a tutar babu; ba lada ba la'ada.

Ga mai son ƙarin bayani zai iya duba waɗannan littafan:
1- Al- Muqtafã fil waqfi wal ibtidã Na Abu Amrinid- Daanjy.
2- Al- Muwãfaqãt da Al- Fatãwã na Abu Ishãq Ash- Shãďibiy.
3- At- Tibyãn Na An- Nawawiy.
4- Talbiisu Ibliis Na Ibnul Jawziy.
5- Bida'ul Qurrã'i Na Bakar Abdullahi Abu Zayd.
6- Albida'ul Amaliyyah Al- Muta'alliqah bil Qur'anil Kareem ،Na Muhammad Ãlu Abdilkareem.

ALLAAH YASA QUR'ANI YA ZAMA HUJJAH GARE MU BA HUJJAH AKAN MU BA.

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
November, 2015.
Post a Comment (0)