MATSAYIN ZAKKA A SHARI'ANCE 17

_*⚖️MATSAYIN ZAKKA A' SHARI'ANCE⚖️*_(17)

ZAKKAR BASHI: 

Wanda kudinsa suka kai nisabi amma sai ya zama da bashi a kansa gwargwadon wannan kudin ko kuma ya tauye nisabin, to babu zakka a kansa. 

Sai dai idan yana da kadara wadda za ta iya biyan bashin.

 Idan kuma mutum yana bin bashi to a dayan biyu yake:
ko dai bashin ya zama ya dade,
ba shi da Karfin zaton zai same shi, to wannan ba zai fitar masa da Zakka ba, sai sanda ya karba.

 Kuma zai fitar da ta shekara daya ne kawai, a sanda ya karba ko kuma bashin ya zama ba mai dadewa ba ne, to in ya zo lissafi sai ya hada da shi ya fitar masa da Zakka.

 Amma fa ya kamata mu sani cewa, bashi ba ya hana fitar da Zakkar dabbobi ko ta amfanin gona, matuKar sun kai nisabi. 

(Duba Fawakihud-dawani sharhin Risala, sh: na 341 – 343)

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*ALHUSEIN ABBAN SUMAYYA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Post a Comment (0)