FARFESUN TALIYAR HAUSA DA NAMAN KAZA


*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*


*FARFESUN TALIYAR HAUSA DA NAMAN KAZA*

Assalamu alaikum, Uwargida A yau na kawo muku yadda ake farfesun taliyar hausa da naman kaza domin magance mura a wannan lokacin. Ina son jawo hankalinku cewa wannan irin farfesun ana iya yinsa ga wanda ya farfado daga rashin lafiya. Kamar mace mai jego wadda aka yi wa aiki sakamakon haihuwa da dai makamancinsu. Wannan farfesun na da armashi sosai domin yana taimakawa majinyacin cin abinci. Sannan masu lafiya ma za su iya shansa domin more irin sinadaren da aka girka da shi. Yana kuma taimaka wa wajen magance mura.

*Abubuwan da za a bukata*
 
· Bata cokula biyu
· Ganyen kori
· Yankakkiyar karas
· Yankakkiyar albasa kamar rabin kofi
· Ganyen ‘thyme’
· Kayan kamshi
· Kowace magi wadda aka yi da dandanon kaza
· Kaza daya
· Taliyar hausa ko ta ‘indomie’
· Romon kaza
· Barkono
· Garin Tafarnuwa

*Yadda ake haɗawa*

A wanke kaza sannan a zuba mata yankakkiyar albasa da gishiri kadan har sai ta nuna sosai ta yi laushi. Sannan a dora tukunya a wuta a narkar da bata sannan a zuba yankakken karas da yankakkiyar albasa da yankakken lawashi a dan soya samasama. Sannan a zuba ganyen ‘thyme’ da magin mai dandanon kaza.

A debo romon kaza sannan a zuba a ciki har sai ya tafasa sannan a zuba garin tafarnuwa da dakakken barkono sannan a rage wuta sai a zuba taliyar hausa a ciki sannan a rufe na tsawon minti 20, sannan a sauke shi da romoromonsa ana sha ana taunar namar kaza da taliya.


*✍Written by admins*
        *Sumayya &*
        *Fauziyya*

*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
      *WhatsApp Group*
      *0814 899 2840*
      *0818 900 7071*
Post a Comment (0)