JININ CIWON HAILA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Jinin Ciwo Na Haila (Istihada)_*

Wani jini ne wanda yake kwarara kuma baya tsayawa, ko kuma wani lokaci yana tsayawa na dan kwanaki kamar kwana daya ko biyu a ckin wata.

*_Alamomin Jinin Ciwo (Haila)_*

= Jinin ciwo ja ne.
= Jinin ciwo. tsinkakke ne.
= Jinin ciwo yana kwarara
= Jinin ciwo bai hamami, amma wani lokacin yana saba ma wadannan alamomin.

*_Tanbihi (Abin Lura):_* Hailanta zai kasance akan abin da akasani na alamomin haila kamar haka;

1. Jinin ya zama baki.
2. Jinin ya zama mai kauri.
3. Jinin ya zama mai hamamin.
4. Jinin ya zama mai tunmuda. To duk lokacin da wadannan alamomin suka kasance sai a tabbatar masa da hukunce hukuncen haila.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)