BARKA DA DAWOWA GIDA MALAM BELLO YABO


*BARKA DA DAWOWA GIDA MALAM BELLO YABO* 

Ahlus Sunna a Nigeria shi ne wanda yake aiki da Hadisan Annabi (saw) tare da bin Alƙur'ani, kuma bai kasance Ɗan Ɗariƙa ko Ɗan Shi'a ko Ɗan Boko Haram ba.

Daga cikin babukan da Hadisan Annabi (saw) suka zo da yawan gaske, akwai babin mu'amala da shugabanni. In ka cire babin Tsarki da Sallah, wannan babin yana daga cikin babukan da Hadisai masu yawa suka zo suna bayani a kansa. Saboda haka bai kamata a ce Ahlus Sunna ya manta da waɗannan Hadisai ko ya jahilce su ba.

A cikinsu Annabi (SAW) ya shiryar da mu yadda za mu mu'amalanci shugabanni, saboda ya san al'ummarsa sun zo ne a ƙarshen zamani, lokacin da kwaɗayin abin Duniya zai yawaita, ake neman mulki da faɗa a kansa ido rufe. Kuma da ma mulki da dukiya su ne suke janyo fitina a tsakanin mutane, har ya kai ga zubar da jinane da asarar rayuka da haifuwar fitina a tsakanin al'umma.

Annabi (SAW) ya nuna mana cewa; za a samu shugabanni masu ƙirƙiro munanan abubuwa, masu aikata munanan aiyuka, masu ɓarna a bayan ƙasa, masu canza sunnoni da keta Shari'a, masu zalunci da zubar da jinane, masu ƙwace haƙƙokin talakawa da wasoson dukiyar al'umma. Amma duk da haka sai ya ce: *MU YI HAƘURI,* mu roƙi haƙƙokinmu a wajen Allah, su kuma shugabanni mu ba su haƙƙokinsu na ɗa'a a kan dadai, sai dai in sun tilasta mana aikata mummuna, to ba mu da laifi a kan haka.
«إنكم سترون بعدي أثرة وأمورا تنكرونها» قالوا: فما تأمرنا يا رسول الله؟ قال: «أدوا إليهم حقهم، وسلوا الله حقكم»
صحيح البخاري (9/ 47)، صحيح مسلم (3/ 1472)

"Lallai a bayana za ku ga zaluncin shugabanni da munanan abubuwa daga gare su".
Sai suka ce: da me za ka umurce mu ya Manzon Allah?
Sai ya ce: "Ku ba su haƙƙokinsu, ku roƙi Allah naku haƙƙokin".

Kuma ya ce:
«إنكم ستلقون بعدي أثرة فاصبروا حتى تلقوني على الحوض»
صحيح البخاري (9/ 47)، صحيح مسلم (3/ 1474)

"Lallai a bayana za ku haɗu da zaluncin shugabanni, amma ku yi haƙuri har sai kun haɗu da ni a tafkina".

Haka kuma Annabi (saw) ya nuna mana cewa: tsinuwa da zagi tsakanin shugabanni da talakawa alama ce ta sharri ba alheri ba.
«خيار أئمتكم الذين تحبونهم ويحبونكم، ويصلون عليكم وتصلون عليهم، وشرار أئمتكم الذين تبغضونهم ويبغضونكم، وتلعنونهم ويلعنونكم»
صحيح مسلم (3/ 1481)

"Mafi alherin shugabanninku su ne waɗanda kuke sonsu suke sonku, suke muku addu'a ku mu kuke musu. Mafi sharrin shugabanninku kuma su ne waɗanda kuke ƙinsu suke ƙinku, kuke tsine musu, su ma suke tsine muku".

Kuma ya koyar da mu hanya mafi dacewa ta kawar da mummunan aiki, mu kawar da hanu idan muna da iko, kuma in ba zai haifar da fitina ba. Ko da baki idan akwai iko, shi ma idan ba zai haifar da fitina ba, ko mu ƙi a zuciya.

Kuma fa Nasiha ake so a yi, ba "Fadhiha" (tona asiri da cin mutunci) ba. Nasiha ita ce: mutum ya yi amfani da hanya mafi kyau don ganin mai kuskure ya gyara.

Saboda haka saɓa waɗannan Hadisai saɓa ma Sunna ce, kamar saɓa Sunna a Hadisan Sallah da Azumi da sauran babukan Addini.

Amma duk da haka, mu ba ma cewa; wanda ya tsine wa shugaba ko ya yi masa Nasiha a kan mimbari shi Bakhawarije ne. A'a, sam ba Bakhawarije ba ne. Shi Ahlus Sunna ne mai kuskure. Saboda Bakhawarije shi ne mai kafirta dukkan Musulmai ya halasta jinanensu, kamar yadda Boko Haram suke yi. Duk wanda ba ya kafirta Musulmai ya halasta jinanensu, shi ba Bakhawarije ba ne. Kamar yadda mutum ba zai zama kafiri idan ya aikata zina ko ya bar wani wajibi ba, haka ba zai zama Ɗan Bidi'a idan ya saɓa wata Sunna da ta zo cikin wani Hadisi ba. Sai dai ya zama Ahlus Sunna mai kuskure da saɓa wasu sunnoni.

Ala ayyi halin, duk shugaba mai iko ba a gyara shi da ƙarfi, a hankali ake binsa. Kuma abin da yake wajibi a kanmu a lokacin zaluncinsa shi ne haƙuri, da yi musu addu'ar shiriya da gyaruwa, a maimakon tsine musu. Shi shugaba komai lalacewarsa, da shi Allah yake tare manyan bala'i masu iya ganin bayan al'umma.

A yi Nasiha, a yi addu'a, a ƙara hakuri, a bi Sunna, sai Allah ya gyara mana su, a samu sauƙi, a yi rayuwa mai daɗi.
Post a Comment (0)