ME KE BATA AZUMI
- Ridda, wato fita daga Musulunci.
- Ci ko sha da gangan ba tare da uzuri ba.
- Haila ko Nifasi, sai dai a kirga kwanakin da aka sha a rama su bayan Ramadan.
- Jima'i, Tarawa da mutum ko dabba ko ma da menene.
- Fitar maniyyi dan sha'awa ko da jima'i ko babu.
- Kakaro amai da gangan.
- Hauka.
Da sauransu.
Idan namiji da mace zuka sadu da rana a cikin watan Azumi to, azuminsu ya baci, sai su rama kuma su yi kaffara.
Don fadin Abu Huraira (R.A) ya ce, wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune sai wan mutum ya zo ya ce, ya Rasulullahi, na halaka, sai Annabi ya ce da shi, mai ya halaka ka? Sai ya ce, na sadu da matata a cikin watan Azumi da rana, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, za ka sami abin da za ka ’yanta bawa? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, za ka iya yin Azumi watanni biyu a jere? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, shin za ka sami abin da za ka ciyar da miskinai sittin? Sai ya ce, a’a, sai mutumin ya zauna a wajen Annabi har aka kawo wa Annabi buhun dabino. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, dauki ka yi sadaka da shi, sai ya ce, ai duk cikin Madina babu wanda ya fi ne bukata. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi dariya har sai da hakoransa suka bayyana. Sannan ya ce, dauki ka je ka ciyar da iyalanka.” (Jama’a da yawa ne suka rawaito).