*MUSULMIN DA YA FI KOWA HASARA 😭*
🌴BALLIGU ANNI no. 218🌴 03/05/2020
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Hasararre a cikin al'ummata shine wanda zai je ranar Alkiyama da (ladan) sallah, da azumi, da zakkah, amma (a duniya) ya (taba) zagin wannan, ya yiwa wannan kazafi, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan. Sai a biya wannan daga ladansa, wannan ma daga ladansa (wadanda yayiwa wadancan abubuwan sai a biyasu da ladan ayyukansa), idan kyawawan ayyukansa suka kare kafin a gama hukunci akansa, sai a dauko zunubansu sai a dora masa, sannan a jefashi cikin wuta".!
📚 Muslim, Hadisi na 4806
👉🏻 Wannan shine yayi ibada amma ladan ake bawa wadanda yake yiwa Qazafi, yake zaluntarsu, dss. Kuma shine wanda wasu za su aikata zunubi amma shi za'a dorawa zunubin! Wannan shine hasararre. Don haka mu kiyaye harshenmu 🤐wajen abinda muke fada akan wasu.
https://t.me/Balligu_Anni