SALLAR IDI DA HUKUNCINTA 1

_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_

       _*SALLAR IDI DA HUKUNCINTA*_
       ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                 _*FITOWA TA 'DAYA*_

_Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

     ```ME AKE NUFI DA SALLAR IDI```
    ➖➖➖ ➖➖➖➖➖➖➖
_*Sallar Idin Azumi* Sallace da Ake Aiwatar da Ita A Farkon Watan Shawwal Bayan Kammala Ibadar Azumin Watan Ramadan Guda Ashirin da Tara (29) Ko Talatin (30). Ana Kiran Wannan Rana da *Idi* Ne Saboda Zagayowa da Takeyi a Kowace Shekara. Kuma Domin Tana Zagayowa da ne da Farin Ciki da Annashuwa Ga Al'ummar Musulmai._

_Addinin Mu Yazo Mana da Bikin Idi Ne Domin Musanyashi da Bukukuwan Idin da Akeyi a Lokacin Jahiliyya, Idin Musulmai Ya Kasance Shi Kadaine Zai Wanzu Kamar Yanda Yazo a Hadisi:_
عن ﺃﻧﺲ ﺑﻦ ﻣﺎﻟﻚ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ : ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ : *" ﻛﺎﻥ ﻷﻫﻞِ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴَّﺔِ ﻳﻮﻣﺎﻥ ﻓﻲ ﻛﻞِّ ﺳﻨﺔٍ ﻳﻠﻌﺒﻮﻥ ﻓﻴﻬﻤﺎ، ﻓﻠﻤَّﺎ ﻗﺪِﻡ ﺍﻟﻨَّﺒﻲُّ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠَّﻢ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔَ ﻗﺎﻝ : ﻛﺎﻥ ﻟﻜﻢ ﻳﻮﻣﺎﻥ ﺗﻠﻌﺒﻮﻥ ﻓﻴﻬﻤﺎ ﻭﻗﺪ ﺃﺑﺪﻟﻜﻤﺎ ﺍﻟﻠﻪُ ﺑﻬﻤﺎ ﺧﻴﺮًﺍ ﻣﻨﻬﻤﺎ : ﻳﻮﻡُ ﺍﻟﻔﻄﺮ ﻭﻳﻮﻡُ ﺍﻷﺿﺤَﻰ“*

_An Kar6o daga *Anas bn Malik (ra)* Lallai Yace: Mutanen Jahiliyya Sun Kasance Sunada Kwanaki Biyu a Kowace Shekara da Suke Bukukuwansu da Wasani a Cikinsu. A Yayin da Manzon Allah (ﷺ) Ya Iso Madina Sai Yace: *“Kun Kasance Kunada Kwanaki Biyu da Kuke Wasanni a Cikinsu, Hakika Ubangiji Ya Musanya Muku da Mafiya Alkhairinsu: Sune Idin Azumi da Idin Layya”*._

_Yana Daga Cikin Abinda Ke Wajaba Akan Musulmi Ya Bayyana Farin Cikinsa a Wannan Ranaku Tare da Bayar da Kyaututtuka Ga Kananan Yara Don Sanyasu Cikin Nishadi da Annashuwa._

_*Sallar Idin Azumi* Itace Farkon Idin Musulmai Wacce Take Zuwa Kafin Idin Layya. Ana Gudanar da Idin Azumi Ne a Daya Ga Watan Shawwal, Sannan Idin Layya ta Biyo Baya wacce Akeyinta a Goma ga Watan Zul-Hijjah. Ana Kiran Idin Azumi Ne da *Idil Fidr* Saboda Wannan Ranar Itace Rana Ta Farko da Musulmai Suke Cin Abinci da Shan Abinsha da Jima'ai da Rana Bayan Sunyi Wata Daya Cir Ba Tare da Samun Wannan Daman ba. Saboda Hakane Ma *Manzon Allah (ﷺ)* Ya Hana Yin Azumi a Wannan Rana ta Idin Azumi. Hadisi ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_
عن ﺃﺑﻲ ﻋﺒﻴﺪ ﻣﻮﻟﻰ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺑﻦ ﻋﻮﻑ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : *”ﺷَﻬِﺪﺕُ ﻋﻤﺮُ ﺑﻦَ ﺍﻟﺨﻄَّﺎﺏِ ﻓﻲ ﻳﻮﻡِ ﺍﻟﻨَّﺤﺮِ، ﺑﺪﺃَ ﺑﺎﻟﺼَّﻼﺓِ ﻗﺒﻞَ ﺍﻟﺨﻄﺒﺔِ، ﺛﻢَّ ﻗﺎﻝَ : ﺳَﻤِﻌْﺖُ ﺭﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋﻠﻴﻪِ ﻭﺳﻠَّﻢَ ﻳﻨﻬﻰ ﻋﻦ ﺻﻮﻡِ ﻫﺬﻳﻦِ ﺍﻟﻴﻮﻣﻴﻦِ، ﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻟﻔﻄﺮِ ﻓَﻔِﻄْﺮُﻛﻢ ﻣﻦ ﺻﻮﻣِﻜُﻢ ﻭﻋﻴﺪٌ ﻟﻠﻤﺴﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺃﻣَّﺎ ﻳﻮﻡُ ﺍﻷﺿﺤﻰ ﻓَﻜُﻠﻮﺍ ﻣﻦ ﻟﺤﻮﻡِ ﻧﺴُﻜِﻜم“.*

_An Kar6o Daga *Abi-Ubaidah Maula Abdulrahman bn Auf (ra)* Yace: Naga *Umar bn Khaddab (ra)* a Ranar Idin Layya, Ya Fara Yin Sallah Kafin Yayi Khudubah Sannan Yace: *“Naji Manzon Allah (ﷺ) Yana Hana Azumtar Wadannan Ranaku Biyu: Amma Ranar Idin Azumi, Ranace da Zaku Bude Bakin Azuminku, Kuma Idi Ga Musulmai. Amma Ranar Ranar Idin Layya, To Kuci daga Abin Yankanku”*._

            _*LOKACIN SALLAR IDI*_
            ➖➖➖➖➖➖
_Lokacin Sallar Idi Yana Farawa Ne Yayin da Rana ta Dan 'Dago Kadan. Wannan Shine Mazhabin Malikiyya da Hanabila da Shafi'iyya kuma da Hanafiyya._

_Hakika Ya Tabbata A Sunnah Lokacin Sallar Idi Yana Farawa ne Lokacin Hantsi Har Zuwa Lokacin da Rana Tayi Zawali. Abinda Yafi dacewa Shine A Gaggauta Yin Sallar a Idin Layya, Sannan a Jinkirtata a Idin Azumi. Wannan Shine Abinda Jamhur Suka Tafi Akanshi Kuma Shine Zantukan Malaman Malikiyya._


_Anan Zan Dakata Sai Mun Hadu a Rubuta Na Gaba_

*سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن الإله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك*

_*✍🏼Sulyman Yahya*_
      _{Abu Aysha Almaliky}_

*📞+2347055883010*

*Zaku Iya Bibiyar mu a Shafin Facebook ta Wannan Adireshin👇🏽👇🏽*
https://www.facebook.com/groups/222507361428028/

_*Ko A Telegram Ta:*_

https://t.me/joinchat/OOh5_RUljMIixFLQgNCDyg


Post a Comment (0)