ZAN IYA BADA KUDI, A MAIMAIKON ABINCI A ZAKKAR FIDDA-KAI ?
Tambaya
Assalamu alaikum Dr. shin ana iya bada kudi azakatul fitr maimakon kayan abinci ???
Amsa
Wa alaikum assalam,
Annabi S. A. W ya wajabta zakkar fidda-kai sa'i na dabino ko Sha'ir Kamar yadda ya zo a hadisin Ibnu Umar wanda Muslim ya rawaito a lamba ta (2287).
Abin da Malamai suka fahimta a hadisin da ya gabata shi ne ana fitar da zakkar fiddakai ne daga abin da mutanen garinku suka fi ci kamar Shinkafa Dawa Masara a wajan 'yan Nigeria.
Fukaha'u sun yi sabani game bada kudi a maimakon abincin da ya zo a hadisi :
1. Umar Dan Abdulaziz da Abuhanifa da Ibnu-taimiyya da Albani da wasu magabata sun tafi akan halaccin bada kudi a maimakon zakkar fiddakai saboda abin da yasa aka shar'anta zakkar fiddakai shi ne: wadatar da talakawa daga barin roko a ranar IDI hakan kuma yana tabbata ta hanyar bada kudi ko kimar abincin.
2. Ya wajaba a fitar da abincin da mafi rinjaye suke ci, saboda Tun da Annabi SAW ya fadi sunayen abinci, hakan sai ya nuna su yake so a fitar ba kimarsu ba, kamar yadda yake a hadisin Ibnu Umar Wanda ya gabata.
Zance na biyu ya fi inganci saboda bin sunnar Manzo shi ne daidai, tare da cewa in an samu lalura ta karancin abinci ko kuma talakawa suka nuna sun fi bukatar kudi ya halatta a fitar da kudin ko kimar abincin a maimakonsa, saboda akwai hadisai da suke nuna halaccin amsar kima a babin zakkar dabbobi in SA'I bai samu dabbar da ya kamata ya amsa ba.
Don neman Karin bayani duba: Al-mabsud 2/156 da kuma Al'istizkaar 9/346 da kuma Al'iktiyarat Alfiqhiyya lil'Albani na Abu-shady shafi na 209-210
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
13/6/2018