*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//28📿*
*GINSHIQI NA 27*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
HANYAR GYARA
Mun yarda da cewa wane ya saki hanya a maganganunsa ko a ayyukansa? Amsar ita ce "I" to shiriya yake buqata yanzu, galibin wanda yake sakin hanya gani yake kamar ya fi ka zama daram a kanta, sai dai a hankali in ka nuna masa kuma aka yi dace da shiriyar Ubangiji sai ya ga kuskurensa ya karbi gyaran, to kai mai gyaran in ka sami mai kuskure a tsakiyar 'bata kar ka matsa ta kowace hanya sai ya bar kuskuren nan take, ka bi a hankali, ba buqatarka a ce ka fadi gaskiya komai dacinta albashi mutum ya tafi da kuskurensa ba, ko kai ne kadai kake iya gaya wa wane gaskiya kai tsaye, a'a, burinka dai shi ne a bar kuskuren a koma kan abinda yake daidai.
A wani hadisi na Anas bn Malik yake cewa: Wata rana muna zaune a masallaci tare da Annabi SAW kwatsam sai wani baqauye ya shigo ya kama fitsari, nan take sahabbai suka yi masa ca! "Kai! Kai!!" Sai Annabi SAW ya ce "Kar ku katse masa fitsarin ku qyale shi" nan take suka fita harkarsa, da ya gama sai Annabi SAW ya kira shi, ya ce masa "Ba a fitsari ko qazanta a irin wadannan masallatan, don ambaton Allah SW da salla da karatun Qur'ani aka yi" sai ya sa wani ya zo da bokitin ruwa ya watsa (Muslim 285), Annabi SAW zai iya cewa a tara masa gajiya don gobe kar ya qara, ko don wani ya gani ya shiga taitayinsa.
Amma hanyar da yake bi wurin magance matsala hanya ce mai sauqi da rashin matsantawa, a zahiri ma da an matsa masa din in ya yanke fitsarin zai cutu, kuma qila da an far masa fitsarin zai watsu a wurare, ko ya bata mutane gaba daya, amma da aka bar shi ya kammala a tsanake an iya magance matsalar gaba daya, kuma shi baqauyen ya ga sassaucin muslunci don a ruwayar Tabaraniy da Haithami ya ce masu ruwayar ingantattu ne ya ce: Da Annabi SAW ya tambaye shi "Me ya sa ka yi mana fitsari a masallacimmu?" Ya ce "Na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya na zata wuri ne kawai kamar sauran wurare shi ya sa na yi... (At-Tabarani a Al-Kabir 11552, 11/220)"
Darasin dake cikin hadisin da yawa gaskiya, don ba ma rashin son cutuwarsa ko kar ya bata wasu ba har ma da nuna masa irin sassaucin dake cikin muslunci, shi ya sa ma a (Sunani Ibn Maja 428) baqauyen ya ma yi wata iriyar addu'a kafin ya kai ga yin firsarin inda ya shiga wurin Annabi SAW ya ce: Allah ka yi mani gafara ni da Muhammad kadai banda sauran, Annabi SAW ya fahimci wani irin mutum ne tun lokacin, kuma ya yi hukunci daidai da yadda ya dace da irin mutumin, haka ake duba mai kuskure a yi hukunci daidai da yadda yake.
*GINSHIQI NA 28*
To idan kuskure ga dan adam ya bayyana me ya kamata mu yi? Zancen gaskiya shi ne gaggawarmu wajen fadin wane ya yi kuskure ba tare da tanadar yadda za a gyara kuskuren ba, har ma ka sami mai yawo da shi a ko'ina "Wane ya yi kaza" a zahirin gaskiya ba a yi wani shiri na masamman game da gyran ba, da kamata ya yi qaunar gyaran ta shiga gaban komai, matsalolin da mafi yawan masu da'awa suka sami kansu kenan a yau, da farko dai mun fahimci wa'azi da tsoratarwa kan mummunar abu ne kawai, alhali akwai kwadaitarwa ma zuwa ga kyakkyawan abu, a gaya wa mutane wasu abubuwan da in suka shiga cikinsa zai kawar da kan su su yi nesa da mummunan.
Na biyu kuma akan tsaya kawai wurin gaya wa mutane ne cewa wane ya yi kuskure ko ya aikata haram, ba tare da tunanin hanyar da za a bullo masa ya tuba ya shiriya ba, kamar dama batarsa ake so, shari'a kuwa ba haka take bi ba, da ta so haramta rìba sai ta halasta rÃbá, yadda mutum bai da zabi sai dai ya bar cin riba din, ta halasta aure ta haramta zina, ta halasta nau'o'in nama na ni'ima ta haramta wasu masu cutarwa, ta halasta zuma ta haramta giya, da haka in mutum ya abka sabo da kauce hanya kuma to a gefe ga wata hanya da zai bi ya tuba.
Shari'a ta ba da qofa ga duk wani abu, ko azumi da ya haramta cin abinci ko jima'i da rana ya bar dare ga kuma ninkin lada, shi ya sa galibin uwayemmu suke son diyoyinsu su yi azumi a dakunansu, mu riqa nema wa kammu sauqi, wani malami dake cewa matsalarmu a yau ba ma bambance kalmar Fatawa da Da'awa, ya yi bayani mai gamsarwa duk mun gane.
Ya ce "Mai fatawa ya kan fadi hukuncin da ake buqata ne a lokacin na mas'alar da ake ciki ko wace aka tambaye shi, takan yi daidai da da'awa wajen sakawa a ma'auni don lura da mas'alar da kuma yanayin mutunen wuri da al'adarsu, amma da'awa akan so a fadi saqon da za a tura ne, a kuma tabbatar saqon ya kai inda ake so, a kuma yi qoqari wurin ganin an yi aiki da shi, wannan ya sa Allah SW ya ce "Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka cikin hikima da kyakkyawan wa'azi" ma'ana ba fadin kawai ba, saqon ya isa inda ake so, kuma a yi aiki da shi. Allah ne masani.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
*Follow my Facebook Page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp