*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*
*SEASONINGS AND SPICES //5*
*21. Cardamom:* Shima kwaya ne da ake amfani dashi wurin girki, yawanci shima a wuraren India ake samun shi, amma yanzu Malaysia da Tanzania suna shuka shi. Shima yana da amfani a lafiyance kamar hana jin amai, zafin kirji, taimako wurin realising gas, kuma yana taimakawa kidney wurin fitar da abun da bashi da amfani a jiki.
*22. Fenugreek (hulba):* Spice ne wanda yan south Asia suke sanya shi a cikin girki, amma a nan dai amfanin da muke dashi daban gaskiya, don masu sashi a girki basu da yawa. Amfanin sa basu da adadi amma ga kadan, idan ana shafa oil din a nono yana tada su ya qara musu girma. Ana shan oil din da zuma yana gyara menstruation, yana hana ciwon ciki during menstruation, idan mace tana dafa shi tare da su kanunfari ko kuma zallan sa tana tsarki yana kashe infection sosai haka ma shan oil din. Dama sauran su gasu nan dayawa.
*23. Cummin:* Shima a family parsley yake, ana amfani dashi a qamshin abinci, ana sashi a dakakke ko kuma a yanda yake.
*24. Turmeric (Curcuma longa):* Turmeric ya banbanta da curry, curry leaves ne shi kuma wannan a qasa ake ciro shi kamar ginger wato a ginger family yake, yana sanya girki yellow da qamshi, yawanci dalilin da yasa ake amfani dashi kenan. Turmeric shine the most powerful spice dake fighting diseases. Pain killer ne shi, yana mutuqar gyara skin, kumburi, diabetes gasu nan dayawa.
*25. Negro Pepper (kimba):* Ana sanya cikin spices especially farfesu zaki hada shi tare dasu citta da kanunfari haka nan in zaki yi yaji.
*26. Scallion ko Spring Onions (Lawashi):* Shima in bamu manta ba ko yaya kika sashi a girki yana bada qamshi sosai. Zaki iya siyan shi ki busar sai daka ki rinqa amfani dashi.
*27. Chives:* Na ga wasu suna kuskuren ce ma chives lawashi gaskiya they two are different things, lawashi bashi da flower a qarshen sa shi kuwa chives akwai flower a qarshen ganyen sa. Shi ma din ana amfani dashi ne a abinci kamar lawashi don in ma ba ka sani ba banbance shi da lawashi a abinci zai maka wuya. Zaku gansu dogayen turawa na sashi a girki.
*✍Written by admins*
*Sumayya &*
*Fauziyya*
*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
*WhatsApp Group*
*0816 772 2658*
*0803 466 1023*
