*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*
*SEASONINGS AND SPICES //4*
*16. Gram Masala:* Idan kika ji ance gram masala ba wai wani spice bane guda daya, a'a ana nufin mix of spices wanda mafiya yawan masu amfani dashi sune yan Indian, Pakistan da sauran su. Ke ma zaki iya hada naki dayawa wuri daya ki kira shi Gram Masala.
*17. Paprika:* Ba wani abu bane illa garin tattasai. Suna amfani dashi don ya sanya girkin su ja kamar yanda muke amfani da namu. To garin sa shine Paprika.
*18. Chilli ko Chille* powder: Shine garin tsidifin da kika sani dai na gida. Ba sai na fada miki a me zaki sa ba.
*19. Coriander/Cilantro:* Wasu suna dauka akwai alaqa tsakanin Coriander da parsley. Wato Corriander seed sune ya'yan wanda ake amfani da powder din shi a girki. Amfanin sa a bangaren lafiya shine yana dauke ne da dietary fiber, vitamins A, C, E, K, calcium, iron, potassium, and magnesium. Wanda in bamu manta ba vitamin k yana taimaka wurin building strong bones, haqora da gashi. Yana rage cholestral da high blood pressure.
*20. Parsley:* Parsley kuma shine ganyen Corriander, wato fresh ganyen Corriander shine parsley duk da wasu sun samu sabani cewa they are two different things. Wato Corriander daban parsley ma daban kuma nima na yarda da hakan don hatta ganyen su da banbanci. Sannan parsley ba shine lansir ba gaskiya sun dai yi kama ne amma wasu sun ce bashi bane. Parsley yawanci garnishing abinci ake yi dashi. Parsley shima ba daga baya ba yana controlling cancer, diabetes etc.
*21. Basil leaves:* Ganye ne shima da ake amfani da danyen ko busashen a girki, Shima yana fighting cancer, viruses da infections, kumburi, gyaran skin dama sauran su.
*✍Written by admins*
*Sumayya &*
*Fauziyya*
*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
*WhatsApp Group*
*0816 772 2658*
*0803 466 1023*
