TAMBAYA TA 140


TAMBAYA 1,722
Assalamualaikum malam barkada yaw nashe malam dokene in kazo wankan hayla say ka sepe gashi kafin kayi wanka nagode
AMSA
Wannan masa'alar tana da maganganu guda biyu a wajen malamai :
1. Wajibi akunce kitso a wajen wankan haila da na biƙi amma banda na janaba wanda kuma hujjarasu anan shine hadisin da bukari ya rawaito hadisi na 317 da muslim 1211 wanda Aisha (ra) tace ranar arafa ta riskeni ina da janaba sai na kai kukana zuwa ga annabi (saw) sai yace min ((ki bar umarar ki, ki kunce kanki ki tsefe sannan kiyi niyyar aikin hajji))
2. Mustahabbi ne a kunce kitso domin wankan haila da na biƙi saboda hadisin da imam muslim ya rawaito daga Aisha hadisi na 311 wanda labari ya riski Aisha (ra) cewa Abdullahi ɗan Amru yana cewa idan mata za suyi wanka dole sai sun tsefe kitsonsu, tace abun mamaki a wajen Abdullahi ɗan amru yana umartan mata dasu kunce kitsonsu lokacin wanka mai yasa bazai ce su aske kansu ba, na kasance ina wanka tare da annabi a kwarya ɗaya bana wuce na kwarawa kaina ruwa sau uku.
Sannan malamai sukace babu hujja ga malaman farko saboda wanka na harami ne, sannan haka na malamai na biyu domin wankan na janaba ne 
*a taƙaice*
Jumhurin malamai sukace mustahabbi ne ba dole bane mace idan zatayi wankan haila ko biƙi ta kunce kitsonta amma a wankan janaba zatayi ne kai tsaye ba sai ta kunce kitson ba saboda hadisin Aisha dake sama da kuma wahalarwa idan akace duk lokacin da janaba ta sameta sai ta kunce.
Wannan bayani na cikin linnisa'i faƙaɗ
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib
Post a Comment (0)