```Assalamualaikum
Don Allah malam, tambayata itace inason cikakken bayani kan sunan "Rabi'atu"```
_*AMSA:*_
*******
ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،
Sunan *"Rabi'atu"* yana nufin wacce aka Haifa tana ta hudu ga iyayen ta, kenan tanada yayye uku.
Sunan *" Rabi'atu"* yayi fice a duniyar Musulmai tin lokacin da sunan wata baiwar Allah (Saliha, Abida, kuma kamammiya mai tsananin tsoron Allah, kuma sarauniyar hikima da salon zance mai cike da wa'azantarwa) ya fara shahara a qarni na biyu na musulunci, sunan wannan baiwar Allah shine *"Rabi'atu Al-Adwiyyah"* tarihi ya zo a _Bidayatu wan-nihaya_ cewa an haife ta a garin *Basra* na kasar *Iraqi* a shekara ta 100AH bayan hijrah kuma ta rasu tana da shekaru 80 a duniya. Allah yaji qanta da rahama.
Daga lokacin ne duniyar musulmai suka kwadaitu da rada wa 'ya'yan su mata sunan *"Rabi'atu"*
*Imam Az-Zhahabi* yace: *Rabi'atu Al-Adawiyyah* ta kasance mai tsananin bautar Allah da tsantseni.
_*(Al-Siyar, 8/241).*_
*Abu Sa'eed Ibn Al-Araby* ya ruwaito gameda *Rabi'atu Al-Adawiyyah* cewa, mutane sun samu kaso mai girma na hikimomi daga gareta.
*Sufyaan, Shu'bah* da *sauransu* sun ruwaito cewa maganar da ake yadawa akanta cewa wai ita tayi addu'a Allah ya bata tsananin kyawon jiki da fata ta yadda mutane zasu rikice daga kallanta, wanda hakan yasa har ta mutu da shekaru 80 jikinta yana kamar na matashiya, *Sufyaan, Shu'bah* da *sauransu* sukace wannan zancen karya ne.
*Imam Al-Dhahabi* yace wannan qagaggen labari ne da jahilci. Yace wata-kila wadanda suka jingina wannan zuwa gareta sune suke da wadannan dabi'u sannan suke so suyi amfani da ita domin su karfafi kafircin su.
Sannan babu wata ruwaya ingantacciya da ta nuna *karamomi* ga *"Rabi'atu Al-Adawiyyah".* Saidai an samu ruwayoyi da suka tabbatar da kalamanta na hikima da bautar Allah (S.W.T), kamar lokacin da tace da *Sufyaan al-Thawri* _"Kai ba komai bane face kwanaki yan kadan, kuma idan kwana daya ya shude wani sashen ka ya tafi. Bada jimawa ba idan sashen ka ya tafi dukkanin ka ka tafi. Kásan da haka, saboda haka kayi aiki akan hakan"._
*Abdah Bint Abi Shawwal,* wacce take daya daga cikin bayin Allah mata nagari kuma mai yiwa *Rabi'ah* hidima, tana cewa: *"Rabi'ah"* ta kasance tana sallah a tsawon dare, sai kusan fitowar Al-fijir sannan ta dan yi angaje har zuwa fitowar Al-fijir, idan ta farka sai tace _*"Ya ke rayuwa ta har tsawon wane lokaci kike barci? Har tsawon wane lokaci kike gyangyadi? Bada jimawa ba zakiyi barci wanda bazaki farka ba har sai ranar da ake tayar da Matattu (Qiyaamah)"*_
*Abdah* tace wannan shine dabi'ar *Rabi'ah* har zuwa rasuwar ta.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*🌙Tambayoyin*_ _*Musulunci🌙*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
_*+2347068043652*_
_*+2348164884055*_