TARIHIN GANIN WATA A NIJERIYA A WATANNI GOMA DA SUKA WUCE


*Tarihi Ganin Wata a Najeriya a Watanni 10 da Suka Wuce*
 
✍️ Salihu Muhammad Yakub, Memba, Kwamitin Dubin Wata na Kasa
3 ga Shawwal 1441H
26t ga Mayu 2020

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

Makasudin wannan rubutu shi ne mu san shin watan Ramadan ne kadai ya taba cika 30 talatin a Nigeria?

Za mu yi amfani da rahoton National Moon Sighting Committee daga Farkon Wannan Shekara ta 1441.

1. Jum'ah 30 ga Agusta 2019.
Wannan ranar ita ce ta zo daidai da 29 ga Dhul Hijjah 1440.
A ranar *Kwamiti ba su samu ganin wata ba*, sai ya zama Assabar 31 ga Agusta 2019 shi ne cikon 30 ga watan Dhul Hijja 1440. 
Lahadi 1 ga September 2019 ya zama 1 ga Muharram 1441.

2. Lahadi 29 ga September 2019. Shi ne 29 Muharram 1441. *Kuma aka ga wata*. Don haka Litinin 30 ga September 2019 ya zo dai dai da 1 ga Safar 1441.

3. Litinin 28 ga October 2019 shine 29 Safar 1441. 
*Ba a ga wata ba*
Talata 29 ga October shi ne 30 Safar 1441. Laraba 30 ga October 2019 ya zama 1 ga R. Awwal 1441.

4. Laraba 27 ga November 2019 shi ne 29 ga R. Awwal 1441. *An ga wata*
Alhamis 28 ga November 2019 shi ne 1 ga R. Thani 1441. 

5. Alhamis 26 ga December 2019 shi ne 29 ga R. Thani 1441.
*Ba a ga wata ba*
Jum'ah 27 ga December 2019 ya zama 30 ga R. Thani 1441. 
Sai Assabar 28 ga December 2019 ya zama 1ga J. Awwal 1441.

6. Assabar 25 ga January 2020 shi ne 29 ga J. Awwal 1441.
*Ba a ga wata ba* Lahadi 26 ga January 2020 ya zama 30 ga J. Awwal 1441. 
Litinin 27 ga January 2020 ya dai dai 1ga J. Akhir 1441.

7. Litinin 24 ga February 2020 shi ne 29 ga J. Akhir 1441.
*An ga wata* 
Talata 25 ga February 2020 ya zama 1 ga Rajab 1441.

8. Talata 24 ga March 2020 shi ne 29 ga Rajab 1441. 
*Ba a ga wata ba*
Laraba 25 ga March 2020 ya zama 30 ga Rajab 1441. 
Sai 26 ga March 2020 ya yi daidai da 1 ga Sha'aban 1441.

9. Jum'ah 22 ga April 2020 ya zama 29 ga Sha'aban 1441 

*Abin lura:* A wannan shekara watanni 5 ne suka yi kwana 30 tun daga Dhul Hijja na karshen shekarar bara. Ga su kamar haka:
1. Dhul Hijja ذو الحجة ya yi 30.

2. Safar صفر ya yi 30.

3. Rabi'ul Akhir 11 ربيع الآخرة ya yi 30.

4. Jimada Ula جمادى الأولى ya yi 30.

5. Rajab رجب ya yi 30.
 
Tambaya:
Mine ne matsala idan Ramadhan ya yi 30?
Ina masu jayayya suke a lokacin da National Moon Sighting Committee suke fidda sanarwa kan wadannan watannin?
▫️Ko sun yarda da sanarwar ne amma na Ramadan ne ba su yarda ba?
▫️Ko kuma basu yarda ba amma sukayi shiru suka ki yin magana?
▫️Ko kuma ba sa bibiyar maganar ganin wata sai Ramadan ya zo?

*Nasiha:*
 🌼 Mu rika yi wa kanmu adalci mu bar kowane aiki ga masu yin sa.
Allah ya yi mana muwafaqa.
🌼 Duk wanda yake so ya dace da daidai a wajen ganin wata to dole ne ya zama yana bibiyar shigowar ko wanne wata da fitar shi
🌼 Ba'a taba zama daidai tsakanin wanda yake fita duba wata koyaushe da wanda sai Ramadan yazo sannan ya fara surutu
🌼 Watanni da yawa sun cika 30 a wannan shekara kamar yadda muka gani a sama.
Post a Comment (0)