*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//14📿*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
*Misali:-*
Malam Raziy ya rubuta a (Al-Mabahith Al-Mussharqiyya) inda ya yi bayani gwargwadon iko, Ibn Taimiyya ya yi masa raddi sosai, har ma ya yi wani littafi inda ya warware duk maganganun da ya yi kuskure a ciki, ya saka masa suna (Bayanu Talbisil Jahamiyya) wanda ya kai sifili goma, duk dai yana maganar manhajinsa ne da aqidarsa, amma a qarshe maganar da ya yi a kan Razi din tana da dadin ji matuqa, akwai adalci da lura da dalilin ma da ya sa ya yi qudurin nasa littafin, asali ba manufa ce ta batar da mutane da jefa su halaka ba, amma tunda akwai barnar dole a warware ta ba tare da taba mutumcinsa ba.
Ya wanke Razi da cewa "Wannan fa ba da gangan ya yi don ya taimaka wa barna ba, ya yi ne gwargwadon abinda zai dace da qwaqwalwa, wajen karatunsa da bincikensa, in qwaqwalwarsa gwargwadon fahimtar da ya yi ta ba shi cewa ya soki wani abu wanda 'yan falsafa suka fada take zai soke shi... daga cikin mutane akwai wanda yake munana masa zaton cewa da gangan yake abkawa cikin bata, wanda sam ba haka ba ne, ya yi magana ne gwargwadon iliminsa, fahimtarsa da bincikensa a duk abinda zai fadi (Fataawa 2/490).
Ibn Taimiyya kenan Allah ya yi masa rahama, shi da kansa yake kore cewa da gangan Razi yake abkawa cikin bata, ya kuma tabbatar da cewa malami ne kuma mai bincike, yakan bi abinda ya fahimta ne daidai ko kuskure, mu a yau in ka zauna da daliban ilimi masamman masu tankade da rairayannan take za su ce maka "Wane dan bidi'a ne manta da sha'aninsa" in za su yi magana a kansa ba za su taba ambato alkhairansa da wata qila za su iya sakawa a yi masa hanzari ba, sai dai kura-kuransa, wani sa'in ma ba sa iya sukarsa kai tsaye sai dai su ce walam wane ya ce kaza da kaza a kansa.
To dubi Ibn Taimiyya bayan ya fadi matsayin Abu-Hamid al-Asfarayini game da Alqali Abubakar Al-Baqalani inda ya yabi Baqalani din ya fito da kyawawan abubuwansa duk da cewa shi ne jagoran masu tawili a wannan lokacin ya ce "Tare da abubuwan da yake da su manya-manya na falala da kyawawan dabi'u masu yawa, ga raddi a kan 'yan dadi arna da wadanda ba su da addinin ma da 'yan bidi'a, kai ya kai ga ba wanda ya fi shi daraja a duk cikin mabiya Ibn Kilab da Ash'ari samsam, ba wanda ya fishi tsara magana, dalilinsa wannan maganar ta yadu (Al-Majmu 28/188-189).
Zahabi yake magana a kan Hakim (Muhammad bn Abdillah Ad-Dabbi An-Naisaburi Al-Hakim, Abdullah Al-Hafis wanda yake da At-Tasanif) ya ce: Malami ne mai gaskiya sai dai a cikin littafinsa yana inganta hadisan da ba su da makama, yana ma yawan yin hakan, ban sani ba ko ilimin gano hakan ya buya masa ne amma ba jahili ne da zai kasa ganowa ba, in dai da saninsa ya yi haka to ba shakka ha'inci ne mai girma, sannan kuma dan Shi'a ne, amma bai taban manyan sahabbannan (Abubakar da Umar).
Ibn Tahir yake cewa na tambayi Abu Isma'il wato Abdullahi Al-Ansari game da Hakim Abu-Abdullah ya ce "Malamin hadisi ne amma fa mugun Barafile ne" sai Zahabi yake cewa "Na ce: Allah yana son adalci ba Barafile ba ne dan Shi'a ne kawai" daga irin maganganunsa cewa da ya yi "Jama'a sun hadu kan cewa Dabbi maqaryaci ne, cewarsa Annabi SAW an haife shi cikin farin ciki ne [Ba kamar sauran mutane dake zuwa suna kuka ba], cewarsa Aliyu RA ne Annabi SAW ya yi wa wasici da zama khalifa bayansa, amma gaskiyarsa a ransa, da iliminsa a fannin lamari ne da aka tabbatar da haka, ya rasu a shekara ta 405 hijiriyya (Mizanul I'itidal 7804).
Zahabiy yake cewa "Duk wanda ya kafurta a dalilin wata babbar bidi'a da ya yi ba kamar kafirin asali ba ne, ko Bayahude ko Banasare ko Bamajushe, Allah ba zai sanya wanda ya yi imani da Allah da manzonsa da ranar Lahira, ya yi azumi, ya yi salla, ya yi hajji, ya yi zakka sai kuma ya yi manyan laifuka, ya bace, ya abka bidi'a daidai da wanda ya qi manzon Allah ya yi bautar gumaka, ya shure dokokin Allah ya kafurce ba, sai dai muna neman tsarin Allah daga bidi'a da 'yan bidi'an (Siyaru A'alamin Nubala 10/202) magana ce mai dadi dake rabewa tsakanin musulmin da ya yi aikin kafurci tare da imani da abinda ya tabbatar da musluncinsa da kuma zallan kafirin da bai yi imani da komai ba.
Kafircin wanda ya yi imani da duk rukunnan muslunci amma ya abka ciki ba kamar kafirin haqiqa ba ne, Allah ne masani, amma wannan kafurcin bai fitar da mutum daga addini, kafurcewa ce a aikace, kamar irin nifaqanci a aikace dinnan, Is'haq bn Rahoya (Rahawaihi) yana maganar ilimin Imam Abu-Ubaid Al-Qasim bn Salam ya ce "Allah na son gaskiya, Abu-Ubaid bnl Qasim bn Salam ya fi ni sanin Fiqihu, ya fi ni ilimi (Siyaru A'alam 10/490-509) Ahmad bn Hambal yake magana game da Is'haq ya ce: "Ban tsallake zuwa Khurrasan kamar Is'haq ba, koda dai yana saba mana a abubuwa, ai dama mutane sukan saba wa junansu a wasu abubuwan (As-Siyar 11/358-383)".
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa:Abulfawzhaan*
