TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 15

*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//15📿*

*GINSHIQI NA SHA UKU*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

GIRMAMA ABOKIN RADDI

Ba wanda zai tattauna da wani ya ce bai damu da nasa mutuncin a kare masa ko zubar ba, tunda wajibi ne a kiyaye mutuncinka, kai ma ya wajaba ka kiyaye na wanda kake yi wa raddi, duk wani mai bincike a harkar addini za ka iske cewa yana da mabiya da almajirai, kuma za ka ga ana amfani da fatawoyinsa ta fuskar addininnan gwargwadon yadda ya ba da su a fahimtarsa da gamsuwarsa, magana makamanciyar wannan ta gabata a baya, haqiqa wadannan mabiyan ba za su ji dadin 'barar kubewar kake yi wa malaminsu ba, ko bai saka su su kare shi ba su ma ba za su rasa abinda za su fada a kanka ba, ko a gabanka ko a bayan idonka, amma in ka tsaya a kan ilimi to gasunan ga shi bisimilla.

Idan almajirai biyu suka sami sabani wurin fahimtar nassi ko hukuncin wata mas'ala bai nufin dole daya daga cikinsu batacce ne kuma zai fuskanci uqubar Allah SW, ko kuma ya zama dole mutane su qaurace masa ko muzanta shi a cikin jama'a, ko a tuhume shi da saba wa gaskiya da gangan, sam bai dace ba a munanta masa mu'amala, a wulaqanta shi, don kawai ya saba maka a fahimta ko wani hukunci, don mutum biyu da suka sami sabani a wurin fahimtar wata shari'a ko hukuncinta bai nufin wani ya fi wani, hukuncin duk da ya zo daidai da shari'a shi ne ya fi, don haka dole a girmama juna, kowa zai iya yin daidai, kamar yadda zai iya yin kuskure.

Ba laifi a zauna a tattauna cikin fahimtar juna, a yi musayar ra'ayi don dai a qarshe a isa zuwa ga gaskiyar, a kuma kauce wa wasu lafuzza wadanda za su iya harzuqa mutum, don akwai lafuzzan da matuqar za a yi aiki da su tabbas ran mutum zai baci, wasu wulaqanta mutum ake yi da su a zubar masa da qimarsa, bai kamata almajiri ko dalibin ilimi ya yi wa dan uwansa dalibi haka ba, wai don kawai ya saba masa a fahimta, kamar ka ce masa "Jahili, dan bidi'a, gafalalle, dan ikhwan tare da sanin bai cancanci dayansu ba, kai ko ma ya cancanta din ai jawo shi kake so ba tunkude shi ba.

Duk mutumin da za ka baqanta masa rai da irin lafuzzanka zai yi matuqar wahala kuma ka ce ka fada masa ne don kawai ya ji dadi ya karbi gaskiya a wurinka, lokacin da Allah SW ya aiki Annabi Musa AS ya ce masa shi da dan uwansa su yi wa Fir'auna magana mai dadi, ita magana cikin taushin murya kan sa a karbi fahimtar mutum, kishiyar hakan kuma kan hana mutum ya karbi gaskiya koda ya gan ta kuwa, na taba jin wani na cewa "In dai gaskiya a bakin malam wane za ta fito, to wallahi gwara na zauna haka, don ba zan taba fahimtarta ba" ban san me ke tsakaninsu ba.

Shatubi ke cewa: Gazali ya fadi a wani littafinsa "Tsanani da zafin wasu masu fadin gaskiya suka sa jahilci ya tabbata a zukatan mutane, sun bayyana gaskiyar ne da sifar qalu-bale da kaurin harshe, suka riqa yi wa masu raunin da suke yin magana da su kallon qasqanci, wannan ya sa su kuma suka kunna wutar gaba a tsakaninsu, suka riqa saba musu a komai, har mummunar aqidar ta tabbata a zukatansu, su kuma malaman dake bi a hankali cikin hikima da dadin harshe suka kasa kawar da abinda wadancan suka yi, duk kuwa da bayyanar barnar qwaro-qwaro (Al-Muwafaqaat 4/265)"

Gazali yake cewa "Duk yadda suka kaurara harshe dole su gaza samun abinda suke so, don matsawar ke sanya aqidar mutum ta tabbata a cikin zuciyarsa, duk dai kuskuren malaman da ba su san kan abin ne ba, sukan matsa tilas sai an amshi gaskiya, su riqa kallon wadanda suka saki hanya da kallo na wulaqanci... ya zama a qarshe ba abinda suke so sai nasara, suna ta qoqarin tabbatar wa mutum abinda suka liqa masa [In suka ce dan Ikhwan ne sai su dage sai sun tabbatar masa da Ikhwanancinnan a dole, koda ya barranta kansa da aqidar, a maimakon su kama hanyar da za su fizgo shi baya masamman yadda ya tsame kansa da aqidar da suke jingina masa].

Ya ce "Da a ce sun bi ta hanyar tausasawa, da tausayi, da nasiha a kebance ba ta matsawa da qasqanci ba da sun yi nasara" ya nuna hakan da cewa "Tunkude mutane ga barin addini da tilasta su su guje wa sauran 'yan uwansu musulmai, wannan kan sa mutane su fuskanci halaka, bidi'a kuma ta tabbata a zuciyoyinsu (Ihya'i Ulumuddin 1/141) duk dai maganganun ba su wuce girmama wanda ake magana da shi ba tare da tabbacin tsarkake niyya, ba tsarkake kai da dada tunkuda mutum zuwa ga halaka ba.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa:Abulfawzhaan*

Post a Comment (0)