TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 16


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//16📿*

*GINSHIQI NA GOMA SHA HUDU*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

BAN DA YI WA WANI HUKUNCI

Galibin abinda muke fama da shi a yau: Da zarar an ce wane ya yi kaza sai ka ji mun fara mamaki "Ashe haka yake ba mu sani ba?" An saki hanyar Allah tun daganan, kamata ya yi a yi bincike, shin ya fada din? A wani irin yanayi ya fadi? Tare da wa? Akwai abinda ya hanga ne ko haka kawai ya fadi? Duk ababan kulawa ne, duk lokacin da za a yi wa wani hukunci akwai buqatar tabbatar da abinda ake zargi a maganganunsa ba magana daya ba, a lura da aqida da kuma matsayi, sannan a lura da hukunci a aqidar da yake bi ko mazhabarsa ba ta wanda suke saba masa ba, tunda har za ka yi wa mutum hukunci to dole ka hau matsayin alqali.

Shi alqalanci ba a yinsa kara zube sai da sheda, da jin ta bakin wanda ake tuhuma, ko wanda zai maye makwafinsa, duk wani fandararren masani ko marubuci za a ji ta wurinsa ne kai tsaye ko wanda zai maye makwafinsa, kamar su rubuce-rubucensa kenan, littafansa, faya-fayensa, da wani karatu da aka dauka a waya ko a redio, wannan shi ne adalcin da aka yi mana umurni da shi ((In za ku yi magana ku yi adalci koda kuwa ga makusanci ne, ku cika alqawarin Allah, da wannan ya yi muku wasiyya don lalle ku wa'azittu (An'am 152)), sai a fadi inda ya yi daidai da inda ya yi kuskure, ba wai a tsaya a kan kusakurensa kadai ba, wannan kam zalunci ne wato rashin adalci.

Don haka yi wa mutum hukunci bai yuwuwa sai an bijiro da kyawawansa inda ya yi daidai da inda ya yi kuskure, sai a yi masa hukunci a kan inda ya fi rinjaye, duk da cewa za a yi qoqari a san yanayin yadda yake fito wa mas'ala, da manhajinsa, da irin lafuzzan da yake amfani da su don ba su ma'anonin da shi yake nufi (Misali: Gayu a tsakaninsu wani kan ce "Shege dan iska, Kai! Zan ci uwarka fa!" Wannan ashar ne, mummunan magana kuwa, amma fa ba wai wanda ya fadi din ba hatta wanda aka fadi masa bai fahimci lafuzzan da wannan munin ba, kowani rukuni da lafuzzansu).

In ya yi magana za a duba komai nasa, a duba yadda yake amfani da lafuzza a littafansa, khudubarsa da wasu laccoci in yana da su, zai iya fadin wata magana wace a zahirinta za a ga cewa ya fandare sosai ma kuwa, amma in aka duba littafansa sai a gano manufarsa a fahimci cewa ba haka din yake nufi ba, misali an ji kamar yana yabon Ikhwananci ne saboda yabon wani shugaba da aka san Ba'ikhwane ne, kamar na ce marigayi Mursi (Allah ya jiqansa), wannan bai sa mu yanke hukuncin cewa "Malam wane Ba'ikhwane ne don ya ce kaza a kan wane" shin akwai Ikhwanancin a karance-karancensa ko rubuce-rubucensa?

Ibn Taimiya yake cewa "Babbar gazawar da muke yi ita ce qoqarin liqa wa mutum kuskure kan abinda ya fada duk da cewa za mu iya gyara zancen, mu tafiyar da shi daidai da yadda aka san mutane suna amfani da shi yau da kullum (Majmu'ul Fatawa 31/113), ya kuma cewa "Daukar fahimtar malamai daga wata magana da suka yi ba tare da an dubo inda suka ciro fassarar maganar ba da yadda suke zaqulo hukunci zai iya sakawa a gina wata mummar fahimta (As-Sarimul Maslul ala Shatimir Rasul p287), wannan adalci kenan, ya isa misali boko haram da muke fama da su a yau, littafan da muke karantawa su suke karantawa, ya aka yi suka samo nasu hukuncin da ya saba wa namu? 

Ba su fahimta ba, ba su nemi malamai su ganar da su ba, sai suka bi nassi a kaikaice suka sami kaikaitacciyar fahimta, ya ce "Dole ne maganar mutum wata ta fassara wata, a dauko maganarsa tanan ta fassara wancan, a fahimci al'adarsa ta ainihi da abinda yake nufi da lafazinsa, in ya yi magana a wani wuri a san zahirin abinda yake nufi, matuqar aka san dabi'unsa za a gane abinda yake nufi da lafazinsa, saninsa din ne zai taimaka, (masu hukunta mutum cikimmu a yau da maganar mutum kawai suke la'akari)"

Ya ce "Amma in ya yi wani lafazi da aka san ba abinda yake nufi da shi ba kenan a maganganunsa duk da haka aka tafiyar da shi a kan haka, zai sa maganganun nasa wani ya riqa dukar wani don ba a dora maganar a kan ma'anar da aka san yana nufi ba, an canza masa magana kenan, an juya manufar an liqa masa qarya (Al-Jawabus Sahih 2/288).

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa:Abulfawzhaan*

*Follow my page.*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)