*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//19📿*
*GINSHIQI NA SHA BAKWAI*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
A YI WA MALAMI HANZARI
Musulmi a duk inda yake yana da buqatar fahimtar littafin Allah, da sunnar ma'aiki SAW, kamar yadda yake da buqatar fahimtar hukunce-hukunce na shari'a, masamman kan abubuwan da suka shafi quduri a zuciya ko wadanda ake yin su a aikace, amma ba a ce dolen-dole kowa a cikin al'umma sai ya san wadannan duka ba, dalilin da ya sa kenan ake buqatar wadanda za su nemo wannan ilimi ta fuskar wajibci, sai su komo su ilmantar da jama'arsu.
Su wadanda suka tafi don nemo ilimin ana buqatarsu da fahimtar nassoshin shari'a, wadanda sai ta su ne za a gane hukunce-hukuncen shari'ar, in mutum ya yi qoqari wajen fidda wani hukunci to fa yana kan dayan al'amura guda biyu: Kodai ya yi daidai ko ya yi kuskure, duk dai alkhairi ne gare shi, in ya yi daidai yana da lada biyu, in ya gaza kuma yana da daya, amma bai da wani zunubi, kenan kuskuren ma da zai yi hadisi ya fadi qarara ba wai ba shi da zunubi ne ba, a'a lada ma za a ba shi, rauni ne Allah ya sani sai ya dubi manufarsa ya saka masa.
Sabanin mu 'yan adam kenan, shi mahaliccinka zai ba ka lada guda na qudurin alkhairi, amma masu fushi da fushin wani, wadanda rayuwa ta hada ku anan duniya har sun kai ka wuta, 'yan Sunna dai sun tafi a kan wannan matsayi na cewa mujtahidi Allah ya yi masa hanzari, in ya yi daidai ko ya yi kuskure, amma mu'utazilawa da Khawarijawa (wato Boko haram) da wasu cikinsu sun yi daidai da ahlus-sunna wal-jama'a da cewa wanda ya yi kuskure a furu'a an yi masa hanzari amma sun saba game da aqida, don nan take sai su kafurta mutum daga ya yi wani dan kuskure qarami.
Ga wanda ya karanta (Amanar rasulu) zai ga addu'o'in da Allah ya fadi a bakin manzonsa, na roqonsa kan cewa kar ya kama mu in mun yi mantuwa ko kuskure, ya ce ((Ubangiji kar ka dora mana irin abinda ka dora wa magabatanmu, kar ka dora mana abinda ba mu da qarfin yinsa, ka yi mana rangwame, ka gafarta mana, ka yi mana rahama, kai ne majibancinmu, ka taimake mu a kan daukacin kafurai Al-Baqara 287)) a hadinsin da Muslim ya rawaito 126, in ya roqi Allah SW, yakan ce masa ya amsa.
Ibn Taimiya ya ce: "Mutum zai iya yin wani tawili a shari'a a kuma gafarta masa duk da haka, idan har ijtihadin irin wanda ake iya yi wa mai kuskure rangwame ne, a kuma qara masa da lada, amma sam bai dace a bi shi a kan kuskuren ba (Iqtida'us Sirat 268), mun dai karanta a baya inda Ibni Taimiya din ya yi wa malam Razi hanzari, ya ce "Manufa dai a san tabbataccen abinda za a yi riqo da shi koda wanda ya bar shi bai ambata ba an yi masa hanzari saboda ijtihadi ne dama ya yi, zai iya zama babban amintacce"
Ya ce "Ba sharadi ba ne amintaccen mutum duk maganganunsa su zama daidai, ayyukansa su kasance Sunna, in aka dora shi a kan haka kenan zai kai matsayin manzo ma (Al-Fatawa 5/561-563) yana fitar da cewa mutum zai iya yin kuskure ya sami lada amma ba zai ci gaba da aikata wannan kuskuren ba, ya kawo maganar mauludi yinsa ba sunna ba ne amma ya ce "Girmama mauludin Annabi SAW, da yinsa duk shekara wanda wani yake yi zai iya yuwuwa ya sami lada saboda kyakkyawar niyya, da kuma girmama Annabi SAW, kamar dai yadda ya gabata maka ne za a iya ganin kyawun aikin wasu wanda yake mummuna a wurin mumini mai kamun kai (Iqtida'us Sirat 282, ka duba 290-294).
Shadubi yake cewa "Bai halasta a dogara da kuskuren malami, ko a yi koyi da kuskuren ba, kamar yadda bai kamata kuma a riqa liqa masa gazawa ba, ko a bata sunansa da ita ba, ba a raina shi saboda wannan, ko a ce shikenan ya bata, wannan duk ya saba wa matsayinsa a addini (I'ilamul muwaqqi'in 3/359), Sa'id bn Musayyab yake cewa "Ba wani babban mutum, ko malami ko saraki sai ka same shi da wani aibi wannan dole ne, amma akwai wasu da ba a fadin kusakuransu sakaka haka... wanda alkhairansa suka fi barnarsa yawa sai a juya wa barnar baya saboda alkhairan (Al-Fatawa 6-258).
Ibn Hajar yake cewa "Malamai kan ce: Duk wanda ya yi tawili akan masa hanzari kuma ba mai sabo ba ne matuqar maganar da ya yi tana kan hanya, kuma sananne ne a fagen ilimi (Adabud dunya waddin p70) na sami wani yana koyar da hadisi sai ya kamo sunan wani babban mutum ka ji ya ce maqaryaci ne, wai lafazin da aka fada kenan, amma fa kalmar a fagen da yadda su wadanda suka fada din a lokacin suke amfani da ita ba ta nufin qarya irin ta yau da muke jinta, ko a tsakankaninmu ba tausasa harshe, haka ake sakinsa gatsar sai dai mutum ya ji shi da haquri ko ya yi abinda zai iya.
Zamuci gaba insha Allah.
*Gabatarwa: Abulfawzhaan*
*Follow my Facebook page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
