SEASONINGS AND SPICES 1

*🍝 GIRKE-GIRKEN ZAMANI 🍝*


*SEASONINGS AND SPICES //1*

Kamar yanda muka sani ne taste wato dandanon abinci shine girki, shiyasa ma yana da kyau ki rinqa tambayar mutane game da dandanon abincin ki, ta iya yiwuwa a bakinki ki ji komai yayi miki amma idan wani yaci sai yaji gyare gyare da dama. Wannan ne yasa wani lokacin in kin riqe wasu spices da mutane dayawa suka yaba to ki riqe su saboda idan kika ce bari in canza sai kuma a sake samun matsala.

Akwai abubuwa namu da ake samu a kusa damu wainda suke mutuqar gyara girki, sai ki duba shin yana da amfani a lafiyance, idan komai lafiya to sai ki riqe ki rinqa amfani dashi. Ga kadan daga ciki da zan jero don qaruwar ki:

*1. Garlic (tafarnuwa):* Tafarnuwa tana taka rawa a jikin dan adam, don haka amfani dashi yana qara lafiya. Tafarnuwa tana kashe qarnin abu, wato idan zaki dafa kifi ko wani abun da ya shafi egg ko gashin kaza ko farfesun shi yana mutuqar inganta su tare da gyara su. Tafarnuwa zaki iya yin garin sa wato ki busar ki daka, ko kuma ki siya duk in zaki yi amfani dashi sai ki saka. Amma dai gaskiya danyen yafi fita saboda busashen qamshin yana sallacewa gaskiya. Sannan ba wai zaki cika bane yanda za a kasa ci ba, a’a dan dai dai yanda wani ma ba zai gane an saka ba, amma kuma zai biya miki buqatar ki na girki. Tafarnuwa yana taka rawa a fannin lafiya, domin yana maganin yeast infection, sannan yana rage duk wani inflammation. Ke ko wuri ne ya kumbura a jikin ki idan kina amfani da tafarnuwa zai rage koma ya tafi gaba daya. Tested and trusted.

*2. Ginger:* A gaskiya macen da ta saki ginger kam tayi babban kuskure a girki, busashen shi muke cema citta, danyen kuma shine ginger. Ginger da muke gani yana taka rawa a fannin lafiya.Yana daya daga cikin the most effective natural remedies, zaki iya shiga internet ki ga amfaninsa. Uwa uba yana mutuqar taka rawa wurin kashe duk qarni na girki, da bada qamshin a girki, duk wanda mace take da shi ta saka, a misali kin zuba shinkafa ko taliya, sai ki dan kankare kadan ki zuba zaki ji canji, ko kuma kiyi blending tare da kayan miya. Sai dai a kiyaye cikashi don zai zama miki yaji.

*3. Kanunfari (cloves):* Yana taka rawa a bangare dayawa, tun daga wurin gashin su hanta da kaza, girki dasu drinks. Shima yana da amfani wurin gyara girki, wasu suna dake shine tare da citta su rinqa amfani dashi. Sannan ke mace ce, ba sai na fada miki irin taka rawar da kanunfari yake yi a jikin ki ba. Yana rage cholestral, yana kashe cutuka, yana maganin tari da sauran infection idan ana sha a tea ko in ana hadiye zallan, shi ko hadiyan shi mace take yana sauko mata da ni'ima da hana gaban ta wari. Haka nan yana tightening mace so kun ga bai kamata mace tayi wasa dashi ba.

*4. Habbatus Sauda (Black Seed):* Mata dayawa basu ma san ana saka habbatus sauda a girki ba don larabawa sun fi amfani dashi, amma shima ana hada shi a cikin spices, wato ki zuba shi a cikin su citta ko tafarnuwa, shi ma garanti daga Manzon Allah cewa tana maganin dukkan cuta, wasu ma suna shansa a tea, sannan yana hana shaidani zama a jikin mutum don shaidanu basa son shi.
Kada mu manta a kullum lafiyan mu shine jarin mu.


*✍Written by admins*
        *Sumayya &*
        *Fauziyya*

*🍝 Girke-Girken Zamani 🍝*
      *WhatsApp Group*
       *0816 772 2658*
       *0803 466 1023*


Post a Comment (0)