TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 21


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//21📿*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

MAGANAR IBN TAIMIYA

Da wani ne ya fadi a zafin kaina dinnan da wahala na karba, amma maganar masu ilimi ce, ya ce "Wanda bai yi wa abokin tauna-taunansa adalci ba, bai yi masa hanzari a kuskuren da ya yi na qoqarin fitar da hukunci ba, a maimakon haka ma sai ya yi wata qatuwar bidi'a, ya qiqiri wata adawa ta yin fito na fito da wanda ya saba masa a fahimta, ko ya kafurta shi, to wannan shi ya zalunci kansa" har zuwa inda yake cewa "Allah yana son magana a cikin ilimi da adalci, yakan qi ta a cikin jahilci, Annabi SAW yana cewa: Alqalai uku ne, biyu na wuta daya na aljanna; Mutumin da ya yi wa mutane hukunci da jahilci wannan yana wuta, da wanda ya san gaskiya amma ya yi hukunci da wani abin, shi ma yana wuta, sai wanda ya san gaskiya kuma ya yi hukunci da ita, shi kam yana aljanna.

Ya ce "An umurce mu da adalci, bai halasta ba idan Bayahude, ko Banasare bare dan Barafide in ya fadi wata magana ta gaskiya a qi karba ko a yi watsi da ita gaba daya, ba za a yi watsi da maganar gaba daya ba sai wace take barna, banda wace take gaskiya (Minhajus sunna 3/343), Ibn Taimiyya ga wanda ya san qiyayyarsa ga Rafidawa ya san adalci kawai yake nema a yi musu ba wai karbar addininsu ko koyarwarsu ba, in a tarihi dan Shi'a ya ce "Sahabbai sun juya baya a yaqin Uhudu" wannan gaskiya ne, in ya yi shiru anan sai a gaya masa cewa ai sun dawo, dawowarsu ma Allah ya ba su nasara suka kori abokan gaban har suka arce a karce nasara ta zama ta muslunci.

An tambayi Ibn Taimiyya akan wanda yake fifita Bayahude ko Banasare a kan Barafide sai ya ce "Alhamdu lillah, duk wanda ya yi imani da abinda Muhammad SAW ya zo da shi ya fi duk wanda ya kafurce masa, koda kuwa wanda ya yi imanin yana da wani nau'i na bidi'a, koda kuwa bidi'ar ta khawarijanci ce, ko ta Shi'a, ko ta Murji'a, da Qadariyya da makamantansu, Yahudawa da Nasara kafurai ne da aka san kafurcinsu a addinin muslunci, shi kuwa dan bidi'a idan yana ganin cewa yana kan daidai ne da abinda Annabi SAW ya zo da shi ba za a ce masa kafuri kai tsaye ba, koda ana ganin yana aikata kafurci to kafurcinsa ba irin na wanda ya qaryata manzon Allah SW ne ba (Al-Fatawa 35/201).

Har ila yau yake kwatanta matsayin alkhairi da sharri yake cewa "Abu mai kyau da mummuna matakai ne da wasu ke amfanuwa da su, su bar abinda suke aikatawa su koma ga wanda ya fi shi, an sami mutane da dama cikin 'yan bidi'annan na musulmai kamar Rafidawa, Jahamiyawa, da ma wasu, a qasashen kafurai, har kafuran da dama suka muslunta a hannunsu, suka amfana ta hanyarsu, sai suka zama musalman 'yan bidi'a, hakan ya fi a ce musu kafurai (Al-Fatawa 13/96), maganar gaba dayanta a kan fifiko ce ba wai a riqi aqidarsu ko a ce za a yi koyi da su a wurin wasu lamuransu na addini ba, abin qyama ne su, musulmi ya guje su, qwarai kuwa, amma in sun yi gaskiya a yi musu adalici kuma ko sun yi kafurci ba irin ta Yahudu da Nasara ba ce bare a ce musu gwara ma kafuran da 'yan bidi'an, na ji masu cewa "Gwara arne da dan Izala" ba aqidarmu ba ce mu ma mu ce gwara arne da wane.

An yi masa tambaya game da aure, shi Ibn Taimiya din, ko za a iya ba su mata, wato Rafidawa Shi'armu a yau, sai ya ce "'Yan shi'annan zalla mutane ne masu son zuciya, ga bidi'a, ga bata, bai halasta ba ga musulmi ya aurar da diyarsa ga dan Shi'a, amma in shi zai auro 'yar Shi'ar yana ganin za ta tuba ya inganta, amma in yana ganin ba za ta tuba ba barin aurenta shi ya fi, ko don kar ta bata masa diyansa, Allah ne mafi sani (Al-Fatawa 32/61), duk wadannan nassoshin na Ibn Taimiyya suna nuni ne kan cewa: Bai kafurta Rafidawa kai tsaye ba, duk kuwa da cewa yana ganin hatsarinsu a tsakankanin muminai ba qarami ba ne.

A haka dai ya yi musu adalci wurin yi musu hukunci, yakan kira su 'yan bidi'a, abinda suke aikatawa kuwa yakan ce masa sabo wanda yake buqatar tuba, ba a cewa kafuri ya yi istigfari, sai dai a ce masa ya muslunta, 'yan Shi'a kuwa cewa ake su tuba su bi addinin Allah kamar yadda aka aiko, duk wanda yake wata aqidar da take warware addinin musluslunci to wannan ba musluncin ba ce, in ta kai ga za a sanya ta a kafurci to ya zamanto akwai bayyananniyar hujja.

Ban taba sanin ana ce wa dan bidi'a ya karbi kalmar shahada don zai komo kan Sunna ba, kamar dai maganar baya ce, sun yarda Akwai Allah, manzon Allah, Qur'ani da sauran littafan Allah, manzanni, sun yarda da qaddara kamar yadda suka yarda da Shahada, salla, azumi, zakka, muna aikin hajji da su, da suna yin wadannan kamar yadda muke yi ba za su karbi wani suna ba, sai dai sun bata, musulmai ne amma fandararru, bai kamata maso shiga aljanna ya biye musu ba, don abinda suke tafiya a kai ya saba wa koyarwar muslunci amma sun fi Yahudu da Nasara.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*

*Follow my Facebook page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)